Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna)

Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna)

Hukumoni a ranar Litinin sun rufe hannu daya na babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria, wacce ke kusa da ginin kasuwar duniya ta Kaduna, bayan wani katon rami ya bayyana kusa da gadar da ke kan hanyar.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, lamarin ya faru ne bayan cunkoson kan titin na ranar Lahadi tare da ruwa mai karfi da aka yi na sama ya kawo fadawar wani katon rami

Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna)
Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna). Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

Babu wanda ya rasa ransa a yayin da lamarin ya faru, ganau ba jiyau ba ya sanar da hakan.

A ranar Litinin, an gano cewa hanya daya ce ke aiki inda jami'an tsaro suka garkame dayar. Jami'an kiyaye hadurran kan titi na tarayya (FRSC) ne suke bai wa masu ababen hawa hannu don sauya hanya.

Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna)
Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna). Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Jerin jiga-jigan APC da ke zawarcin shugabancin jam'iyyar da manyan mukamai

Wani dan achaba mai suna Suleiman Umar, wanda ya zanta da manema labarai, ya ce an sanar da shi cewa ramin ya rufta bayan da wasu manyan motocin siminti biyu suka wuce ta kan gadar.

Ya tabbatar da cewa katon ramin ya janyo babban cunkoson kan hanya wacce ta dakatar da ababen hawan da ke barin jihar ko shiga.

Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna)
Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna). Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

Masu achaba kuwa sun ci gaba da amfani da hanyar da ramin yake amma ta gefen da abun bai shafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel