Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Arewa

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Arewa

  • Wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Akwanga, jihar Nasarawa
  • An yi garkuwa da Safiyanu Isa Andaha tare da wani Alhaji Adamu a yammacin ranar 1 ga Janairu, 2024 a hanyar Akwanga-Andaha
  • Tuni jami'an 'yan sanda da hadin guiwar wasu jami'an tsaro suka fita farautar 'yan bindigar don kubutar da mutanen da suka kama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Nasarawa - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Safiyanu Isa Andaha.

Mai baiwa gwamnan jihar Nasarawa shawara kan harkokin kananan hukumomi da masarautu, Mista Haruna Kassimu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 100 a filato, majalisa ta nemi zama da jigogin tsaro

Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukumar Akwanga
Rundunar 'yan sanda ta bazama neman 'yan bindigar da suka sace shugaban karamar hukumar Akwanga, jihar Nasarawa. Hoto: @NGPolice
Asali: Twitter

Abin da 'yan sanda suka ce kan sace Safiyanu Isa

Kassimu ya ce an sace Safiyanu Isa ne a kauyen Ningo da ke karamar hukumar Akwanga ta jihar tare da wani Alhaji Adamu Custom a yammacin ranar 1 ga Janairu, 2024, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa jami’an tsaro sun kai dauki cikin gaggawa ta hanyar bin bayan ‘yan bindigar da suka gudu tare da shugaban karamar hukumar, sai dai ba a san inda suka kai su ba.

A cewar Tribune Online, kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce jami’an tsaro na nan suna kokarin ganin an sako shugaban karamar hukumar da sauran wanda aka kama.

Sokoto: Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da rundunar tsaro

A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya kaddamar da rundunar tsaron jihar da nufin taimakawa sauran jami'an tsaro wajen magance matsalar tsaro a jihar.

Sai dai gwamnan ya ce bai samar da rundunar tsaron don ta zama kishiyar rundunar 'yan sanda ba, kawai dai ya yi hakan don karfafa tsaro a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.