Sabuwar Shekara: “Dala Za Ta Kai N2,500”, Babban Malamin Addini Ya Hango Abun da Zai Faru a Najeriya
- Shahararren malamin addini a Najeriya, Prophet Ritabbi, ya bayyana abun da Allah ya nuna masa game da shekarar 2024
- Ritabbi ya yi hasashen karin wahalhalu ga yan Najeriya yayin da duniya ta yi maraba da sabuwar shekara
- Malamin addinin ya ce makarantun gwamnati za su rufe "saboda ba za a samu kudin biyan malamai ba"
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jos, jihar Plateau - Wanda ya kafa majami'ar 'Christ as of Old Ministry,' Prophet Ezenwa George Ritabbi, wanda aka fi sani da Prophet Ritabbi, ya ce shekarar 2024 za ta zama ta Kiristoci masu bin gaskiya.
Prophet Ritabbi, a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin cocinsa na Facebook, Godofnownow.tv, ya ce 2024 za ta zama shekara ta musamman ga Kiristoci na hakika.
'2024 zai zama mai muni ga wasu' - Ritabbi
Malamin mazaunin Filato ya yi ikirarin cewa duk abubuwan da wadanda suka yi imani basu samu ba a shekarun baya za su cimmasu a 2024. Sai dai kuma, ya yi hasashen wahalhalu ga wasu mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Prophet Ritabbi ya ce:
"Na fada maku a tsakiyar shekarar nan (2023) shekara mai zuwa (2024) za ta zamo daya daga cikin mafi muni.Amma ga wadanda suke karkashin wannan ni'ima, wadanda suke tafiya cikin gaskiya, zai zo masu da sauki. A nan ne littafin Malachi 3:17-18 zai zo.
"Ina fada masu hasashen abun da zai faru a 2024. Na fada masu cewa Bola Tinubu (shugaban kasar Najeriya) zai siyar da Najeriya sannan ya karbi kudi.
"Sai kun zama masu bin gaskiya don sake gani. Ba yanzu ne lokacin da zan sake ce ma wani ya tuba ba. Yanzu, dole ne, ko ka halaka."
Ya ci gaba da hasashen cewa:
"Za ka kasance da kudinka, kudinka zai zama ba shi da amfani, kamfanoni da dama za su nade; iyaye za su kira taron PTA sannan su ce ba za mu iya biyan wannan ba (kudin makaranta). Duk na ga wadannan abubuwan.
"Gina gida mai dakuna hudu sai ka kashe abun da suka yi amfani da shi wajen gina bene 20.
"Kuna kokawa yanzu, amma dala za ta kai N2,500.
"Gakiya nake fada maku. Na gan shi. Kuna da kudi a banki, ba za ku iya karbarsu ba kuma; sun daskarar da shi.
"Sun gabatar da sabon kudi. An buga sabon kudi, don kawai su sake garkame kudaden mutane a banki.
"Kowani kaya yana haurawa sama sau 10. Kayan gine-gine za su zama wani abu daban."
Kalli cikakken bidiyon a kasa:
Malamin addini ya hararo 2024
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa fitaccen Fasto a Najeriya, Philip Goodman ya yi hasashen shekarar 2024 za a yi ta cikin nasara.
Fasto Goodman ya ce za a samu karyewar farashin danyen mai wanda hakan dole zai saukar da farashin man fetur a kasar.
Asali: Legit.ng