An Ga Tashin Hankali Bayan Direbobin Mota Sun Murkushe Jami'an 'Yan Sanda 2 Da Gan-Gan
- An shiga tashin hankali bayan wasu direbobin motoci biyu sun murkushe jami'an 'yan sanda biyu da gan-gan
- Lamarin ya faru ne yayin da 'yan sandan ke bakin aiki inda suke binciken ababan hawa a jihar Legas
- Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin bai ba da bahasi kan lamarin ba bayan tuntubar sa da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Wasu direbobin mota sun murkushe jami'an 'yan sanda guda biyu a yankin Oshodi da ke jihar Legas.
'Yan sandan na bakin aiki inda suke binciken ababan hawa masu wucewa lokacin da abin ya faru.
Yaushe lamarin ya faru a Legas?
Lamarin ya faru a karshen mako da misalin karfe 7:30 na dare a tashar motar 7/8 da ke Oshodi a Legas, cewar AllNews.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta tabbatar da cewa 'yan sandan sun gamu da tsautsayin ne bayan direbobin mota kirar Toyota Camry' da 'Lexus 350' sun nufo kansu.
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a gano lambar motocin da suka aikata wannan mummunan aika-aika ba.
Lamarin ya faru ne bayan jami'an 'yan sandan sun yi kokarin tsayar da motocin don bincike.
Kamar yadda Punch ta tattaro, majiyar ta ce:
"Yayin da suka hango jami'an 'yan sandan, direbobin sun kara gudu inda suka nufo 'yan sandan.
"Nan take suka murkushe 'yan sandan guda biyu masu suna Sifeta Alabi Kayofe da Sifeta Edukpe Oronya."
A dalilin haka, Sifeta Kayofe ya ji raunaka a kai da kuma hannunsa na hagu yayin motocin duka bi kan Sifeta Oronya.
Mene rundunar 'yan sanda ta ce a Legas?
Direbobin motocin su yi kokarin sace makaman 'yan sandan sai dai ba su yi nasara ba bayan wani dan sanda ya dakatar da su.
Tuni aka kwashi jami'an 'yan sandan zuwa asibitin Divine Grace da ke Mafoluku-Oshodi din ba su kulawa ta musamman.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya ci tura, Street Journal ta tattaro.
Hundeyin ya amsa wayar da aka kira shi amma ya bukaci a tura masa sakin kar-ta-kwana bayan dan jaridar ya gabatar da kansa.
Tinubu ya shiga masallacin Juma'a da Sanwo-Olu
A wani labarin, an yi ta cece-kuce bayan Shugaba Tinubu ya shiga masallacin Juma'a da Gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Sanwo-Olu wanda shi ne gwamnan jihar Legas ya kasance Kirista inda hakan ya ta da jijiyoyin wuya a kasar baki daya.
Asali: Legit.ng