Yadda ‘Yan Majalisa Za Su Kashe Naira Biliyan 344 a Kan Abubuwa 29 a Kasafin 2024

Yadda ‘Yan Majalisa Za Su Kashe Naira Biliyan 344 a Kan Abubuwa 29 a Kasafin 2024

  • Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilan tarayya za su iya batar da abin da ya zarce N300bn a shekarar nan ta 2024
  • ‘Yan majalisar sun yi kari a cikin kasafin kudinsu, za a jira amincewa da sa hannun Mai girma shugaban kasa
  • Idan Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kasafin, za a aikawa majalisa kudinsu yadda doka ta tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Majalisar tarayya ta amince da kasafin kudin sabuwar shekarar nan ta 2024, sai dai an yi kari a kan abin da aka bada.

‘Yan majalisar kasar sun kara kusan N147bn a cikin kasafinsu, Premium Times ta kawo bayanin yadda za su batar da kudinsu.

'Yan majalisa
Wasu ‘Yan Majalisa a bakin aiki Hoto: House of Representative
Asali: Facebook

Rahoton nan ya jero abubuwa, gine-gine da aikace-aikacen da za a batar da kudi a kan su bayan an yi bayanin dalilin yin karin.

Kara karanta wannan

Talakawa na kukan na abinci, an warewa majalisa biliyoyin don siyan littafai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasafin kudin majalisa a 2024

1. Ofishin Majalisar tarayya – N36.7bn

2. Ofishin Sanatoci – N49.1bn

3. Majalisar wakilan tarayya – N78.6bn

4. Hukumar Majalisar Tarayya – N12.3bn

5. Hadiman Majalisa – N20.3bn

6. Kudin ko-ta-kwana – N15.1bn

7. Kwamitin Kasafin kudi a Majalisar dattawa – N200m

8. Kwamitin Kasafin kudi a Majalisar wakilai – N200m

9. Kwamitocin kula da Asusun gwamnati a Majalisa – N280.7m

10. Kudin fara ginin Dakn karatu a Majalisa – N12.1bn

11. Cigaba da ginin Majalisa – N4.2bn

12. Bashin Majalisa – N8.5bn

13. Dakin karatun zamani – N225m

14. Gyaran kundin tsarin mulki – N1bn

15. Kammala ginin NILDS – N4.5bn

16. Ginin NASC – N10bn

17. Ofisoshin Akawu da Manyan Sakatarori – N1.2bn

18. Na’urorin wuta – N4bn

19. Ofisoshin shiyyoyin Majalisa - N3bn

20. Wurin ajiye motocin Sanatoci – N3bn

21. Wurin ajiye motocin ‘Yan majalisa – N3bn

22. Gyaran ofisoshin kwamitin Sanatoci – N2.7bn

23. Gyaran ofisoshin kwamitin Majalisar wakilai – N3bn

Kara karanta wannan

Abin da ya sa mu ka kara Naira Tiriliyan 1.2 a kasafin da Tinubu ya gabatar Inji Majalisa

24. Ginin madaba’ar zamani a Majalisa – N3bn

25. Ginin ofishin bincike da kasafin kudi a Majalisa (NABRO) – N3bn

26. Ginin asibitin Majalisar tarayya – N15bn

27. Wurin shakatawa a Majalisa – N4bn

28. Sayen litattafan dakin karatun Majalisa – N3bn

29. Hukumar fanshon Majalisa – N2.5bn

Ministoci na neman kari a kasafin kudi

Ana da labari wasu mnistoci sun nuna kasafin kudin shekarar 2024 da aka yi ba zai je ko ina ba, sun bukaci majalisa ta kara kasonsu.

Ministan tsaro, Badaru Abubakar ya roki a kara masa kudi saboda tashin farashin dizil da man fetur da aka samu a tsakiyar bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng