Badakalar N37bn: Tsohuwar Ministar Buhari Za Ta Gurfana Gaban EFCC
- Hukumar EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin amsa tambayoyi
- Hukumar ta gayyaci Sadiya Umar Farouq ne domin tatttaunawa da ita kan badaƙalar N37bn a lokacin tana minista
- Sadiya a baya ta fito ta bayyana cewa ba ta da hannu a badaƙalar ta N37bn da ake zargin an haɗa baki da wani ɗan kwangila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati (EFCC), ta gayyaci tsohuwar ministar harkokin jin ƙai, Sadiya Umar-Farouq.
Hukumar ta gayyaci Sadiya ne kan cigaba da gudanar da bincike kan wasu maƙudan kuɗaɗe N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar da su a hannunta ta hannun wani ɗan kwangila, James Okwete.
EFCC ta gayyaci Sadiya
An buƙaci tsohuwar ministar da ta gurfana a gaban masu bincike a hedikwatar EFCC, Jabbi, Abuja a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu, 2024, domin ta yi bayani kan badaƙalar zamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda ta musamman da ta gani a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba.
Wani ɓangare na takardar na cewa:
“Hukumar na binciken wani lamari ne da ya shafi karkatar da kuɗaɗe da ya shafi ma’aikatar kula da jin kai, bala’o’i da cigaban al’umma a lokacin da kike minista."
"Dangane da abin da ke sama, ana buƙatar da ki kawo kanki domin tattaunawa wacce aka tsara kamar haka: Laraba, 3 ga watan Janairu, 2024. Lokaci: Ƙarfe 10:00 na safe."
Me tsohuwar ministar ta ce?
An kasa samun tsohuwar ministar domin jin ta bakinta a ranar Asabar, saboda wayarta ta nuna cewa a kashe take.
Da aka tuntuɓi tsohuwar mai taimaka mata kan harkokin yaɗa labarai, Nneka Ikem kan lamarin, sai ta kashe wayarta.
"Kamar yadda kake tambayata? Nima zan tambaye ka, a ina ka samu labarin cewa EFCC ta gayyace ta? Ikem ta tambaya kafin ta yanke kiran.
Kiraye-kirayen da aka ƙara yi mata ya nuna wayarta a kashe take.
A baya Umar-Farouq ta musanta sanin ɗan kwangilar, James Okwete, wanda har yanzu yana hannun hukumar EFCC.
EFCC Ta Fara Tuhumar Ministocin Buhari
A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta fara tuhumar wasu ministocin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan badaƙalar N187bn.
Ministocin guda uku waɗanda suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Buhari, ana zarginsu ne da wawure dukiyar ƙasa.
Asali: Legit.ng