A Karshe, Majalisar Dattawa Ta Amince da Babbar Bukatar Tinubu da Aka Yi Ta Cece-Kuce, Akwai Dalili

A Karshe, Majalisar Dattawa Ta Amince da Babbar Bukatar Tinubu da Aka Yi Ta Cece-Kuce, Akwai Dalili

  • A yau Asabar, Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Tinubu bukatar sake karbo basukan makudan kudade a kasar
  • Majalisar ta amince da kudade har dala biliyan 7.8 da kuma wasu Yuro miliyan 100 don inganta bangarorin kasar
  • Wannan na daga cikin tsarin basukan da Gwamnatin Tarayya take son karba daga shekarar 2022 zuwa 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Majalisar Dattawa ta amince wa Shugaba Tinubu don sake karbo bashin dala biliyan 7.8.

Har ila yau Majalisar ta kuma bai wa shugaban damar sake cin Yuro miliyan 100 da ya bukata a kwanakin baya.

Majalisa ta amince da butakar Tinubu na karbo bashi
Majalisar Dattawa Ta Amince da Bukatar Tinubu Na Karbo Bashi. Hoto: Godswill Akpabio, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wace bukatar Tinubu Majalisar ta amince da shi?

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 100 a filato, majalisa ta nemi zama da jigogin tsaro

Wannan na daga cikin tsarin basukan da Gwamnatin Tarayya take son karba daga shekarar 2022 zuwa 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta amince da bukatar shugaban bayan karbar rahoto daga kwamitin basukan kasashen ketare, cewar Trust Radio.

Bukatar shugaban ta samu sahalewar Majalisar ce a yau Asabar 30 ga watan Disamba yayin zamanta a Abuja.

Tun farko Shugaba Tinubu ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta amince da karbar basukan lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Mene dalilin Tinubu na karbo bashin?

Majalisar zartarwar ta amince da karbo basukan ne a ranar 15 ga watan Mayu don inganta harkar noma da kiwon lafiya da kuma tsaro.

Sauran wuraren da basukan za su taba sun hada da harkar ilimi da manyan ayyuka da kuma sauran bangarorin kasar, cewar The Nation.

Tinubu ya ce karbar basukan ya zama dole don samar da kudaden da za su maye gurbin gibin da aka samu a wurin inganta tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito yayin da majalisar dattawa ta shirya amincewa da kasafin kudin 2024

Har ila yau, ya ce za a yi amfani da kudaden don taimakawa tattalin arzikin kasar ya dawo hayyacinsa don inganta rayuwar ‘yan kasa.

A kwanakin naya ne shugaban ya tura bukatar don karbar basukan a wata wasika da ya tura zuwa ga shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.

An yi wa Tinubu ihu a Legas

A wani labarin, wasu matasa a jihar Legas sun yi wa Shugaba Tinubu ihu inda suke cewa 'muna jin yunwa'.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya tafi hutun bikin Kirsimeti jihar Legas da kuma na sabuwar shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.