Hedikwatar Tsaro Ta Bayyana Nasarorin da Sojoji Suka Samu a Shekarar 2023

Hedikwatar Tsaro Ta Bayyana Nasarorin da Sojoji Suka Samu a Shekarar 2023

  • Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar da wani rahoto na ƙarshen shekara kan ayyukan sojojin ƙasar nan a shekarar 2023
  • Rahoton da aka fitar a ranar Juma’a, 29 ga watan Disamba, ya bayyana cewa sojoji sun kama sama da mutum 6,000 da ake zargin ƴan ta’adda ne
  • An kuma tabbatar da cewa an sako sama da mutum 4,000 da aka yi garkuwa da su daga hannun ƴan ta'addan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta sanar da nasarorin da sojojin Najeriya suka cimmawa daga watan Janairu zuwa Disamban 2023.

DHQ ta ce sojojin sun halaka ƴan ta’adda da masu laifi 6,886, sun kama mutum 6,970 da ake zargi, tare da ƙubutar da mutum 4,488 da aka yi garkuwa da su daga watan Janairu zuwa Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tafka sabon ta'adi, sun halaka bayin Allah da sace gomman mutane

Sojoji sun samu nasara a 2023
Sojoji sun halaka yan ta'adda masu yawa a 2023 Hoto: The Nigerian Army
Asali: Facebook

Manjo Janar Edward Buba, daraktan ayyukan yaɗa labarai na hukumar ne ya gabatar da waɗannan nasarori a ranar Juma'a, inda ya bayyana irin ƙoƙarin da sojojin ke yi a faɗin ƙasar nan a lokacin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, sojojin sun ƙwace makamai iri-iri guda 3,320 da alburusai iri-iri har guda 39,075.

Da yake jawabi kan yaƙi da satar ɗanyen mai, Janar Buba ya ce sojojin sun ƙwato litar ɗanyen mai 100,316,600, lita 60,339,426 na AGO, lita 3,465,450 na DPK, da kuma lita 3,544,990 na PMS.

Wane ƙalubale sojojin suka fuskanta?

Duk da waɗannan nasarorin, Janar Buba ya yarda cewa yanayin tsaro a 2023 ya kasance mai ƙalubale, wanda ke tattare da ɗumbin matsaloli.

A kalamansa:

"Wannan yanayin rashin tabbas na barazanar da buƙatar neman zaman lafiya sun cigaba da haifar da babban ƙalubale ga jami’an tsaro."

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

"Saboda haka, dakaru daban-daban sun cigaba da samar da dabaru domin mayar da martani ga waɗannan barazanar."

Kakakin na DHQ ya bayyana cewa, rundunar soji ta duƙufa wajen samar da kayan aikin da suka dace domin tunkarar barazanar da ƙasar nan ke fuskanta.

Sojoji Sun Samu Ƙarin Girma

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar sojojin Najeriya ta yi wa Birgediya Janar 45 ƙarin girma zuwa muƙamin Manjo Janar.

Haka kuma an yi wa sojoji mai muƙamin Kanal 75 ƙarin girma zuwa muƙamin Birgediya Janar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng