Yan Bindiga Sun Tafka Sabon Ta'adi Bayan Sun Halaka Bayin Allah da Sace Gomman Mutane
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyukan babban birnin tarayya Abuja da jihar Neja
- Ƴan bindigan sun halaka mutum huɗu tare da sace mutum 39 a harin da suka kai a ƙauyukan Kuduru, Garam da Azu
- Hare-haren ƴan bindiga suna ƙara yawaita a ƙauyukan birnin tarayya Abuja musamman waɗanda ke makwabtaka da jihohin Neja da Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An kashe mutum huɗu yayin da wasu mutum 39 aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai hari a ƙauyukan Abuja da jihar Neja.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Kuduru da ke ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja da kuma ƙauyukan Garam da Azu da ke jihar Neja, cewar rahoton Daily Trust.
A ranar 23 ga watan Disamba, ƴan bindigan sun kai farmaki Garam, wanda ke da nisan kilomita biyar daga garin Bwari, inda suka kashe wani Fasto na Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) tare da yin garkuwa da wasu mutum 13.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, ƴan bindiga sun mamaye ƙauyen Kuduru a ranar 28 ga watan Disamba, wanda ya yi iyaka da ƙauyen Garam, inda suka yi garkuwa da mutum 18, rahoton TheCable ya tabbatar.
Ƴan bindigan sun tafka ta'asa
Har ila yau, a ranar 29 ga watan Disamba, ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Azu, inda suka halaka mutum uku tare da yin garkuwa da wasu mutum takwas.
Wata mazauniyar Garam, wacce ta bayyana kanta da suna Misis Juliana, ta bayyana cewa:
"Ƴan bindigan sun kutsa wani gida ne, suka yi garkuwa da wasu yara maza guda biyu waɗanda suka kai yi musu jagora zuwa gidan da wanda suka zo nema. Da suka isa gidan sai suka yi awon gaba da mutanen gidan baki ɗaya, amma yayin da suke fitowa daga gidan, sai suka harbe mutumin (wanda suka zo nema), wanda Fasto ne a cocin RCCG, a gaban matarsa da ƴaƴansu uku."
Har yanzu dai rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ba ta mayar da martani kan lamarin ba.
Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sanda
A wani labatin kuma, kun ji cewa aƙalla ƴan sanda biyu ne suka rasa ransu bayan da ƴan bindiga suka kai farmaki a jihar Anambra.
Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da sabbin bindigun AK-47 a yayin harin sun kuma yi garkuwa da mutane da dama.
Asali: Legit.ng