Dalilin Daukar Kudin Kananan Hukumomi 44 Domin Gina Gadoji a Birni Inji Abba Gida Gida
- Abba Kabir Yusuf zai yi amfani da kudin kananan hukumomi domin gina wasu manyan gadojin sama
- Masu suka sun ce babu adalci ayi amfani da arzikin da kauyuka suka mallaka wajen kawata birane
- Gwamnan jihar Kano ya fitar da jawabi wajen kaddamar da ayyukan, ya ce ba yau aka fara yin haka ba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Mai girma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da aikin gida gadojin sama biyu wanda za su ci N27bn.
Ana ta surutu a kan wannan aiki ganin an dauki dukiyar kananan hukumomi duk da a cikin biranen Kano ne za ayi ayyukan.
Daga asusun hadaka na kananan hukumomi da na jiha za a fitar da kudin gadojin saman na Kofar Dan’agundi da hanyar Tal’udu.
Kano: Gwamna Abba ya damƙa ƙananan yara 7 hannun Iyayensu bayan ceto su, ya tura saƙo ga gwamnan Bauchi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ba yau aka fara hakan ba, ya kare gwamnatinsa da cewa wannan al’adar gwamnatocin Kano ne.
A wani jawabi da gwamnan ya fitar a makon nan, yayi bayanin abin da ya sa aka taba kudin sauran kananan hukumomin jihar.
Jawabin da ya fito ta bakin Sanusi Bature Dawakin Tofa ya maida martani ga masu sukar gwamnan da aka fi sani da Abba Gida Gida.
"Wannan ya kasance al’adar magabatana na samar da kudin irin wadannan manya-manyan ayyuka da asusun hadaka na kananan hukumomi da jihohi"
- Sanusi Bature Dawakin Tofa
Bayanin Darekta Janar na yada labaran ya fito a Premium Times a safiyar Asabar.
Kamar dai zamanin Rabiu Kwankwaso, mataimakin gwamnan Kano ne kwamishinan harkokin kananan hukumomi da raya karkara.
Wasu sun nuna ya kamata ne a kashe kudin karkara a samar da ayyukan da ake bukata, amma wasu sun ce kowa zai ci moriyar aikin.
Kotu za su hana Abba aiki?
Kwanaki kotun tarayya ta haramtawa gwamnatin Abba taba kudin da ke cikin asusun jihar saboda rusa shagunan 'yan kasuwa.
Ana haka ne sai mu ka samu labari cewa shugabannin kananan hukumomi sun shigar da kara a kotu domin hana taba masu kudi.
Karar da aka shigar a gaban D.U Okorowo ta bukaci a takawa gwamnatin jiha burki wanda hakan zai iya shafar aikin gadojin saman.
Asali: Legit.ng