Bayanai Sun Fito Yayin da Majalisar Dattawa Ta Shirya Amincewa da Kasafin Kudin 2024

Bayanai Sun Fito Yayin da Majalisar Dattawa Ta Shirya Amincewa da Kasafin Kudin 2024

  • Majalisar dattawa za ta yi zamanta na yau Asabar 30 ga watan Disamba da karfe 1:00 na rana domin tantance kasafin kuɗin shekarar 2024
  • Babban magatakarda na majalisar dattawa, Chinedu Akubueze ne ya sanar da matakin sauya ranar da nufin tabbatar da tsarin kasafin kuɗin na watan Janairu zuwa Disamba na gwamnatin tarayya
  • Shugabancin majalisar ya bayyana ƙudirinsa na zartar da kasafin kuɗin shekarar 2024 kafin ƙarshen shekarar 2023 domin tabbatar da wannan tsarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa za ta fara zama domin tantancewa tare da zartar da kasafin kuɗin 2024 a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba, da ƙarfe 1:00 na rana.

Ku tuna cewa tun da farko majalisar dattawan ta ɗage zamanta har zuwa ranar Juma'a, 29 ga Disamba, domin yin nazari da zartar da kasafin kuɗin shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Cikakkun sunaye sun bayyana yayin da rundunar soji ta samu sabbin janarori 112

Majalisar dattawa za ta amince da kasafin kudi
Majalisar dattawa ta shirya amincewa da kasafin kudin shekarar 2024 Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Sai dai, kuma an mayar da ranar zuwa ranar Asabar 30 ga watan Disamba, kamar yadda wata sanarwa da magatakardar majalisar dattawa, Chinedu Akubueze ya fitar, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattijawa na son kiyaye tsarin kasafin kuɗin Janairu zuwa Disamba

Legit.ng ta tattaro cewa shugabannin majalisar sun bayyana aniyarsu ta zartar da kasafin kuɗin shekarar 2024 kafin ƙarshen shekarar 2023 domin kiyaye tsarin tsarin kasafin kuɗi na watan Janairu zuwa Disamba na gwamnatin tarayya.

Wani ɓangare na sanarwar da Chinedu ya fitar na cewa:

"Ana sanar da sanatoci cewa zaman majalisar dattawa, wanda aka shirya a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba, zai gudana da ƙarfe 1:00 na rana."

Minista Ya Nemi Karin Kasafin Kudi Ga Ma'aikatarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan bunƙasa ma'adanan ƙasa, Dele Alake, ya ce ma'aikatarsa na bukatar Naira biliyan 250 don haƙo ma'adanai amma gwamnati ta ware masa Naira biliyan 24.

Akan bukatar karin Naira biliyan 250, Mr Alake ya ce dole gwamnati ta zama kan gaba wajen hakar ma'adanai, maimakon kyale kamfanoni suna cin karensu ba babbaka a harkar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng