Yan Bindiga Sun Tafka Ta'asa a Abuja, Sun Sace Babban Basarake da Wasu Mutum 5

Yan Bindiga Sun Tafka Ta'asa a Abuja, Sun Sace Babban Basarake da Wasu Mutum 5

  • Ƴan bindiga sun sake tafka ta'asa a birnin tarayya Abuja bayan sun kai wani mummunan hari a ƙaramar hukumar Bwari
  • Ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Pandan-Gwari inda suka yi awon gaba da Hakimin ƙauyen tare da wasu mutum biyar
  • Hakan na zuwa ne dai bayan ƴan bindigan sun halaka mutum uku da yin awon gaba da wasu mutum shida a ƙauyukam Tokulo da Garam na ƙaramar hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan bindiga sun sake kai hari a ƙaramar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja.

Harin na zuwa ne bayan da ƴan bindiga suka mamaye ƙauyukan Tokulo da Garam da ke ƙaramar hukumar, inda suka harbe mutum uku tare da yin awon gaba da mutum shida.

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

Yan bindiga sun sace basarake a Abuja
Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a wani sabon harin da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Pandan-Gwari na ƙaramar hukumar, sun yi awon gaba da Hakimin ƙauyen da wasu mutum biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin ƙauyen Kawu, Israel Musa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:34 na daren ranar Laraba, inda ƴan bindiga masu yawa ɗauke da manyan muggan makamai suka kai farmaki ƙauyen Panda -Gwari da ke kusa da Kawu, inda suka sace Hakimin da wasu mutum biyar.

Ya ce ƴan bindigan sun fara kai hari ne a gidan Hakimin tare da sace shi bayan da suka samu shiga ɗakinsa ta ƙofar baya inda suka yi ta harbe-harbe.

An tattaro cewa mafi yawan ƴan bindigan da ke addabar yankunan karkara a Bwari sun fito ne daga ƙauyukan da ke makwabtaka da FCT da jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mai garkuwa da mutane da ke sayar da yara

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, dangane da harin, sai dai ba ta dawo da amsar saƙon da aka aika mata ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wuta Kan Ayarin Jagoran PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan ayarin motocin jagoran jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Anambra, Chris Uba.

Miyagun ƴan bindigan sun farmaki ayarin motocin ne a ƙaramar hukumar Aguara ta jihar inda suka halaka jami'an ƴan sanda mutum biyu har lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng