Innalillahi: Fitaccen Dan Siyasa Kuma Ambasada Daga Arewa Ya Kwanta Dama, Bayanai Sun Fito
- Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya tura sakon jaje kan rasuwar Ambasada M. Z Anka bayan fama da jinya
- Anka wanda jigon jam'iyyar PDP ne ya rasu ne a yau Juma'a 29 ga watan Disamba bayan ya sha fama da gajeruwar jinya
- Gwamnan a cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Allah ya karbi rayuwar fitaccen dan siyasa a jihar Zamfara, Ambasada M. Z Anka bayan ya sha fama da jinya.
Anka wanda ya kasance dattijo kuma jigon jam'iyyar PDP ya rasu ne a yau Juma'a 29 ga watan Disamba.
Yaushe marigayin Anka ya rasu?
Marigayin shi ne mahaifin kwamishinar Lafiya a jihar Zamfara, Dakta Aisha MZ Anka, kamar yadda Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dauda Lawal ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin inda ya ce an tafka babban rashi.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a yau Juma'a 29 ga watan Disamba, cewar Mediasmartnews.
Gwamnan ya ce mutuwar Anka ta bar babban gibi wanda zai yi wahalar cike wa.
Martanin Gwamna Dauda kan rasuwar Anka
Dauda Lawal ya bayyana Anka a matsayin mutum mai kwarewa a bangarori da dama wanda hakan zai yi wahala a samu gurbinsa.
Ya ce:
"Rashin M. Z Anka ba iya na kusa da shi ba ne kawai suka rasa shi, rashin ya shafi dukkan mutanen jihar baki daya.
"Anka ya rasu cikin tsari da dogewa wanda ya kasance mutum mai kan-kan da kai da gaskiya da kuma jajircewa.
"Gudunmawar da ya bayar a kokarin kafa jihar Zamfara ya tabbatar da tsayawarsa don ganin jihar ta samu ci gaba."
Dauda ya kara da cewa Anka ya kasance shugaba nagari mai nusantar da mutane kuma abin alfaharin jihar.
Ghali Na'Abba ya rasu a Abuja
A wani labarin, tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba ya riga mu gidan gaskiya.
Na'Abba ya rasu ne a ranar Laraba 27 ga watan Disamba a wani asibiti a Abuja bayan fama da jinya.
Asali: Legit.ng