'Yan bindiga Sun Buɗe Wa Ayarin Jagoran PDP Wuta, Sun Tafka Ta'adi Tare da Kashe Rayuka

'Yan bindiga Sun Buɗe Wa Ayarin Jagoran PDP Wuta, Sun Tafka Ta'adi Tare da Kashe Rayuka

  • Yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyu yayin da suka kai hari kan ayarin jagoran PDP a jihar Anambra, Chris Uba
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa ayarin wuta ranar Alhamis da daddare amma jigon siyasan ya sha da ƙyar
  • Wata majiya ta ce tsohon ɗan takarar gwamnan PDP a zaben 2019, Val Ozigbo, ya shaida abinda ya faru da Uba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki ayarin jagoran Peoples Democratic Party (PDP), Chris Uba, ranar Alhamis da daddare.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa maharan sun kai hari kan ayarin babban jigon PDP a kauyen Uga da ke ƙaramar hukumar Aguata a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe yan sanda, sun sace fasinjojin da suka tafi hutun Kirsimeti

Yan bindiga sun farmaki ayarin jigon PDP.
Yan Sanda Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Ayarin Jagoran PDP a Anambra Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Twitter

Duk da ɗan siyasan ya tsallake rijiya da baya a motar sulƙen da yake ciki amma maharan sun yi nasarar bindige ƴan sanda biyu har lahira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa wani dan siyasar da ya tsira daga harin shi ne ɗan takarar Labour Party, kuma tsohon dan takarar gwamnan PDP a 2019 a jihar, Valentine Ozigbo.

Yadda yan bindigan suka buɗe wuta

Wata majiya ta bayyana cewa motocin da ke ayarin Uba, jagoran PDP a jihar Anambra sun sha ruwan harsasai a harin, Leadership ta ruwaito.

Majiyar ta ce:

“Mun gane wa idonmu abin da ya faru, ayarin motocin Chris Uba ne suka durfafi wasu mutane da suka tsaya a mahadar UGA, lamarin da ya kai ga musayar wuta."
"Uba ya samu nasarar tsira ne saboda yana cikin motar da harsashi ba ya iya fasa ta amma ‘yan sandan da ke tare da shi ba su taki sa'a ba, nan take aka kashe su."

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Miyagu sun yi alkawarin sake kai hari bayan kashe mutum 195 a Filato

" Shi kuma Val Ozigbo ya dawo ne daga Owerri tare da iyalansa, kwatsam sai ya ga ayarin motoci sun tunkaro shi da mugun nufi, suna kokarin ture shi, nan take ya sa direbansa ya kauce musu."

Majiyar ta ƙara da cewa jim kaɗan bayan ayarin motocin sun wuce Ozigbo, sai suka faɗa tarkon ƴan bindigan, waɗanada suka buɗe wuta har suka kashe ƴan sanda 2.

"Ozigbo wanda ya yi parking gefe guda a lokacin da lamarin ke faruwa, daga baya ya samu labarin cewa ayarin da maharan suka buɗe wa wuta na Uba ne.”

Mahara sun sake kai hari a jihar Filato

A wani labarin kun ji cewa Miyagu sun sake kai hari wani kauye a karamar hukumar Bakkos kwanaki ƙalilan bayan kashe rayuka 195 a Filato.

Ciyaman ɗin ƙaramar hukumar, Monday Kassah, ne ya tabbatar da harin, ya ce maharan sun kona gidaje amma ba su kashe kowa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262