Yan Bindiga Sun Kashe Yan Sanda, Sun Sace Fasinjojin Da Suka Tafi Hutun Kirsimeti
- Yan sanda sun tabbatar da cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki a wani gari Uga da ke jihar Anambra
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kai harin ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba, inda suka wani jami'i
- Haka zalika, an ruwaito cewa sun yi garkuwa da mutane da dama, yayin da suka mamaye garin tare da yin harbin kai mai uwa da wabi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Anambra - Akalla ‘yan sanda biyu ne ake zargin an kashe tare da yin garkuwa da wasu mutane a ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba, yayin da ‘yan bindiga suka kai farmaki jihar Anambra.
Wani mazaunin garin Uga da ke karamar hukumar Aguata ya yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnan jihar Farfesa Chukwuma Soludo da su ceci rayuwarsu.
‘Yan bindigar kamar yadda The Nation ta tattaro suna dauke da sabbin bindigogi kirar AK-47 inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wani a mahadar Uga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindigar sun kashe jami'an 'yan sanda
Sha tale-talen na kai wa gidan jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Andy Uba da shugaban jam’iyyar PDP, Chris Uba.
Wata majiyar ta ce:
"Yan bindigar sun shigo garin misalin karfe 5:50 na yamma cikin motocin alfarma inda suka bude wuta, a nan ne suka harbe wasu jami'an 'yan sanda guda biyu.
"Hasashen AK 47 sun farfasa tagogin gidan sayar da man fetur na CAPAD, amma baya ga kashe ‘yan sandan biyu, babu wanda ya samu ko rauni a farmakin."
Abin da 'yan sanda ke cewa game da harin
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin
Sai dai ya ce bayanan da rundunar ta samu game da lamarin na da sarkakiya.
Ya ce:
"Da zaran mun samu cikakkun bayanai, rundunar za ta fitar da sanarwar a hukumance."
Sufetan 'yan sanda ya kashe kansa bayan bindige abokin aikinsa a Rivers
A wani labarin, wani Sufetan 'yan sanda, Nelson Abuante ya kashe kansa bayan da aka ce ya harbe abokin aikinsa Monday Gbaramana har lahira a jihar Rivers.
Rahotanni sun bayyana cewa Sufeta Abuante ya harbe abokin aikinsa bisa kuskure, amma ganin barnar da ya yi, ya yanke shawarar aika kana lahira nan take, rahoton Legit Hausa.
Asali: Legit.ng