Sokoto: Gwamna Ahmed Aliyu Ya Kaddamar da Sabuwar Rundunar Tsaro a Jiharsa
- Gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da sabuwar rundunar tsaron al'umma, domin taimakawa sauran jami'an tsaro
- Da ya ke rattaba hannu kan dokar kafa rundunar tsaron, Gwamna Aliyu ya ce rundunar tsaron ba kishiyar 'yan sanda ba ce
- Gwamnan jihar ya kuma ce wannan matakin zai taimakawa gwamnatin Shugaba Tinubu ya tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Sokoto - A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya sanya hannu a kan kudirin dokar samar da jami'an tsaron al'ummar Sokoto.
A ranar 21 ga watan Disamba ne majalisar dokokin jihar ta amince da kudirin gwamnan na kafa jami’an sintiri a jihar.
Da yake rattaba hannu kan kudirin dokar a gidan gwamnati, Aliyu ya ce gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaron don tallafawa kokarin gwamnatin Bola Tinubu na samar da isasshen tsaro ga al’umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manufar samar da rundunar tsaron al'umma a Sakkwato - Gwaman Aliyu
Ya kara da cewa jami'an tsaron al'ummar ba kishiyar ‘yan sanda bane, kamar yadda jaridar The Puch ta ruwaito.
A cewar gwamnan:
"Rattaba hannu kan wannan doka ta samar da jami'an tsaron Jihar Sokoto wani muhimmin ci gaba ne a rayuwar wannan gwamnati.
“Kamar yadda muka sani, jihar Sokoto na fuskantar matsalar rashin tsaro, musamman ‘yan fashi da makami, wanda hakan ke kawo ruguza yanayin zaman lafiya da aka san jihar da shi."
Aliyu ya kara da cewar:
"Kirkirar wannan jami’an tsaro an yi shi ne domin kara yunkurin samar da tsaro na yau da kullun don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Bari in fada a fili cewa jami’an tsaron al’umma ba ‘yan sandan Sokoto ba ne, gwamnatin jihar ba ta kirkiro jami'an taron don zama kishiyar 'yan sanda ba.”
Ya yi kira ga sauran jami’an tsaro da su ba rundunar da ya kaddamar goyon baya domin an samar da ita ne don su taimaka a wannan yunkuri na ganin an samu zaman lafiya.
Gwamnan jihar Katsina ya kaddamar da rundunar tsaron al'umma
A wani labarin, kun ji yadda shi ma gwamnan jihar Katsina, Mallam Umaru Dikko Radda ya kaddamar da dakarun tsaron al'umma a jiharsa.
Gwamna Radda ya ce ya samar da rundunar tsaron ne don yaki da 'yan bindiga, da kuma taimaka wa sojoji da 'yan sanda wajen wanzar da zaman lafiya a jihar Katsina.
Asali: Legit.ng