Harkar tsaro: Jami'an Sokoto, Zamfara, Katsina da Kaduna za su hada karfi

Harkar tsaro: Jami'an Sokoto, Zamfara, Katsina da Kaduna za su hada karfi

- Jami’an tsaron da ke Arewa sun shirya yaki da miyagun da ke Yankin

- Rundunar Sojoji da Takwarorin su za su ga karshen safarar kwayoyi

- Akwai matsalar tsaro a Kaduna da Zamfara da Sokoto da ma Katsina

Gwamatoci da Jami’an tsaro da ke Jihohin Sokoto, Katsina, Kaduna da ma Zamfara na kokarin ganin yadda za su hada kai da juna domin kawo karshen rashin tsaron da ake gani a yankin musamman a ‘yan kwanakin nan kamar yadda mu ka samu labari daga The Nation.

Harkar tsaro: Jami'an Sokoto, Zamfara, Katsina da Kaduna za su hada karfi
Za ayi maganin matsalar tsaro a Arewa maso yamma

Rundunar DSS masu fararen kaya a kasar da Sojoji da ‘Yan Sanda da irin su Hukuamr NSCDC da na NDLEA da gandurobobi sun bayyana cewa su na wani shirin da zai taimaka wajen ganin bayan karshen tsageru da masu satar dabbobi da fashi da makami da garkuwa da mutane.

KU KARANTA: Jama'an Kaduna sun koka da halin rashin tsaro a cikin Gari

Babangida Dutsinma wani babban Jami’in Hukumar NSCDC ya bayyanawa ‘yan jarida cewa yanzu haka su na wani sintiri na Operation Harmony a wuraren da barna tayi yawa. Shi ma dai wani babban Jami’in ‘Yan Sanda DSP Muhammad Shehu ya tabbatar mana da haka.

Jami’an tsaron za su maida hankali wajen kawo karshen satar mutane da ake yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma fashi a hanyar Birnin Gwari da sauran manyan hanyoyi irin su Kaduna zuwa Garin Jos. Har wa yau ana kokarin ganin bayan masu safarar miyagun kwayoyi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng