“Ba a Haramta Siyar da Giya Ba” Gwamna Bago Ya Karyata Rahoton Haramta Siyar da Barasa a Niger

“Ba a Haramta Siyar da Giya Ba” Gwamna Bago Ya Karyata Rahoton Haramta Siyar da Barasa a Niger

  • Gwamnan jihar Niger, Umaru Bago ya ba da umurnin kamo wani Mohammed Ibrahim da ya fitar da sanarwar haramta siyar da giya a jihar
  • An ruwaito Ibrahim ya sanar da cewa hukumar ba da lasisin sarrafa giya a jihar ta haramta siar da giya a kananan hukumomi 9 ciki har da Suleja
  • Sai dai a wani martani, gwamnan jihar ya ce har yanzu ba a kaddamar da hukumar ba, don haka Ibrahim sojan gona ne wanda za a hukunta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Niger - Gwamnatin jihar Niger ta karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa hukumar ba da lasisin sarrafa giya a jihar ta saka dokar haramta sha da sayar da giya a wasu kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan jihar Arewa ya gwangwaje manoma 2,040 na jiharsa, ya yi abin a yaba

Idan ba a manta ba, rahotanni sun nuna cewa wani Mohammed Ibrahim, sakataren hukumar ya fitar da sanarwar haramta sayar da giya a kananan hukumomi 9 ciki har da Suleja.

Ba a haramta sayar da giya a Niger ba
Gwamnan jihar Niger Muhammed Umaru Bago ya karyata rahoton cewa ya haramta sayar da giya a jihar Niger. Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Sai dai gwamnatin jihar ta jaddada cewa Gwamna Mohammed Umaru Bago ya na goyon bayan duk wani kamfani ko dan kasuwa da zai yi kasuwanci a jihar ma damar bai saba doka ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta hukunta Ibrahim Mohammed

A cewar gwamnan, har yanzu ba a kaddamar da hukumar ba da lasisin sarrafa giya a jihar ba, don haka babu dalilin yarda da umurni daga hukumar da ba a kafa ta ba, Leadership ta ruwaito.

Ya ce:

"Ina so ku sani, gwamnan manoma ya ba hukumomin tsaro damar kamo wani Mohammed Ibrahim da ya yi ikirarin shi ne sakataren hukumar da ba a kai ga kaddamar da ita ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Haramta Sha da Sayar da Barasa a Wasu Kananan Hukumomi 9 a Jiharsa

"Muna kira ga al'umma da kafofin watsa labarai su yi watsi da waccan sanarwa da mutumin ya fitar, tare da neman karin bayani wajen jami'an gwamnati idan bukatar hakan ta taso."

An haramta sha da sayar da barasa a jihar Niger?

A wani labari da Legit ta kawo, hukumar ba da lasisin sarrafa giya a jihar Niger a ranar Litinin ta fitar da sanarwar haramta sha da sayar da giya a kananan hukumomi tara na jihar.

Hukumar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakatarenta, Ibrahim Mohammed Bonu, ta ce karamar hukumar Suleja na cikin wadanda dokar haramcin ta shafa.

Ibrahim Bonu ya ce dokar za ta fara aiki ranar 1 ga watan Janairu, kuma akwai gidajen barasa da za a dauke daga Minna zuwa wajen gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.