Matashi Da Ke Zaune a Turai Ya Aikawa Abokinsa da Zai Yi Aure Gudunmawar N3k Kacal

Matashi Da Ke Zaune a Turai Ya Aikawa Abokinsa da Zai Yi Aure Gudunmawar N3k Kacal

  • Wani dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya ya aikewa abokinsa za zai yi aure a gida Najeriya gudunmawar N3,000
  • An rahoto cewa mutumin na a cikin kungiyar WhatsApp da aka bude don tara kudi gabannin bikin wani abokinsu
  • Wani dan kungiyar wanda ya kadu da abun da mutumin ya bayar ya ba da labarin a dandalin X

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani mutumi da ke zaune a Birtaniya ya bayar da gudunmawar N3,000 saboda bikin abokinsa da za a yi a Najeriya.

Wani abokinsu wanda ke a kungiyar WhatsApp da aka bude don karbar gudunmawar bikin ne ya ba da labarin.

Matashi ya turawa abokinsa da ke aure gudunmawar N3k
Matashi Da Ke Zaune a Turai Ya Aikawa Abokinsa Da Ke Aure Gudunmawar N3k Kacal Hoto: Getty Images/Tim Robberts and Bloomberg.
Asali: Getty Images

Da yake ba da labarin a dandalin X, @Fattsoul ya ce wasu mambobin kungiyar sun kadu a lokacin da suka ga gudunmawar da dan Najeriyan mazaunin Birtaniya ya bayar.

Kara karanta wannan

Canjin Naira da wasu matsalolin tattalin arziki 9 da ‘yan Najeriya su ka fuskanta a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga dukkan alamu, a nasu tunanin, gudunamawar da zai bayar zai fi na kowa duba ga cewar a Birtaniya yake zaune.

Ya rubuta:

"Ana ta karbar gudunmawa don bikin wani tsohon abokin aiki. Wani da ke zaune a Birtaniya ya aiko da N3,000.00. Naira Dubu Uku! Shugaban kungiyar na WhatsApp ya tambaye shi ko kuskure ya yi. Mutumin ya amsa da "fitarwar shine babban abu". Sai da aka ba da baki sosai kan kada ayi waje da gayen."

Ga wallafarsa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@adekanye52 ya yi martani:

"Shin kun tambayi mutumin da ke UK ko ya ci abinci?"

@yemajiconcept ya ce:

"Da ma bai aiko da komai ba, mutanen da ke cewa ko dole ne - Bai ma kai Yuro 5 ba. Haba mana. A turai kake fa! duk munin abun, bana tunanin Yuro8 = #10,000 matsalar sa ce. Shakka babu baya so ya bayar ne, toh da bai yi ba."

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

Matashiya ta yi tsadadden siyayya

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata wallafa da ta yi a TikTok, wata matashiya ta ba da labarin kasaitaccen siyayya da suka je ita da kawarta suka yi.

Yan matan biyu sun kashe zunzurutun kudi har naira miliyan 1.9, tana mai cewa suna matukar son kamshi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng