Diyar Akeredolu Ta Fattaki Yan Jarida Daga Gidan Mahaifinta, Ta Bada Dalili

Diyar Akeredolu Ta Fattaki Yan Jarida Daga Gidan Mahaifinta, Ta Bada Dalili

  • Ololade, diyar marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu, ta yi yar dirama yayin da ta fatattaki yan jarida daga gidan mahaifinta da ke Ibadan
  • Yan jaridan sun isa gidan marigayi gwamnan ne saboda ziyarar ta'aziyya da Gwamna Abdulrahman Abdulrasaq da Seyi Makinde suka kai
  • Sai dai diyar Akeredolu ta ce gidan Ibadan gida ne mai zaman kansa ba gidan gwamnati ba ne da yan jarida za su iya mamayewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Diyar Marigayi Rotimi Akeredolu, Ololade, ta fatattaki yan jarida da suka je daukar bayanan ziyarar ta'aziyya da manyan masu fada aji suka kai gidan tsohon gwamnan jihar Ondo a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, diyar tsohon gwamnan ta koka cewa gidan Ibadan gidansu ne mai zaman kansa ba gidan gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: Jerin hadiman gwamna da suka yi murabus daga muƙamansu bayan mutuwa ta gitta

Marigayi Rotimi Akeredolu
Diyar Akeredolu Ta Fattaki Yan Jarida Daga Gidan Mahaifinta, Ta Bada Dalili Hoto: Rotimi Akeredolu
Asali: Twitter

Dalilin da yasa duyar Akeredolu ta fatattaki yan jarida daga gidan mahaifinta

Yan jarida sun kasance a wajen ne saboda ziyarar ta'aziyya da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Abdulrahman Abdulrasaq na Kwara da mataimakinsa, Seyi Makinde na jihar Oyo suka kai gidan marigayi gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, zuwan yan jaridan ya tunzura Ololade, wacce ta umurce su da su bar gidan mahaifinta mai zaman kansa, tana mai bayyana cewa ba gidan gwamnati bane.

Abdulrasaq da Makinde sun isa gidan marigayi gwamnan da ke Jericho a yammacin ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, da misalin karfe 5:30 na yamma.

Yadda gwamnonin Kwara da Oyo suka kwantar da tarzoma a gidan Akeredolu na Oyo

Kai tsaye gwamnonin biyu suka isa gidan inda a nan ne matar marigayi gwamnan, Betty da wasu danginsa suke zaman makoki.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: An rantsar da sabon gwamnan Ondo bayan mutuwar Gwamna Akeredolu, bayanai sun fito

Wasu abokan aiki, sun shiga lamarin tare da yayyafawa lamarin ruwan sanyi yayin da manema labarai da ke bakin kofar shiga gidan suka fusata da abun da ta yi.

A nasu bangaren, gwamnonin sun lura da abun da ya faru sannan suka fice zuwa cikin unguwan inda manema labaran ke jiran jin ta bakinsu, rahoton LIB.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Kwara ya yabawa Akeredolu bisa jajircewarsa wajen ganin ci gaban al'umma a lokacin da yake raye.

Sowore ya magantu kan mutuwar Akeredolu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zabukan 2019 da 2023, ya ce wasu mutane na da hannu a mutuwar tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Da yake magana a wata hira da News Central a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, wanda jaridar Legit ta bibiya, Sowore ya ce idan da a wurin dake aiki da hankali ne, da za a gurfanar da wadanda ke da hannu a mutuwar Akeredolu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng