Yan Bindiga Sun Kai Hari a Babbar Kasuwar Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba da Yan Kasuwa Masu Yawa

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Babbar Kasuwar Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba da Yan Kasuwa Masu Yawa

  • Miyagun ƴan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Taraba bayan sun kai farmaki a kasuwar Gongon Maliki
  • Ƴan bindigan waɗanda suka kewaye kasuwar sun ƙwace kuɗaɗe da kayan abinci daga ƴan kasuwar a lokacin harin
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da ƴan kasuwa waɗanda ba a san adadinsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Wasu ƴan bindiga da ke kan babura a jiya Laraba, sun kai farmaki wata kasuwa ta mako-mako da ke Gongon Maliki, a jihar Taraba.

Ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu ƴan kasuwa da ba a tantance adadinsu ba, tare da kwashe kayayyaki da suka haɗa da kayan abinci na dubban Naira, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun sheke miyagun yan bindiga 6 a jihar Bauchi

Yan bindiga sun tafka ta'asa a Taraba
Yan bindiga sun sace yan kasuwa a Taraba Hoto: Agbu Kefas
Asali: Twitter

Kasuwar Gongon Maliki tana ƙaramar hukumar Yorro ne a jihar kuma tana ci ne a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin ya auku

Ƴan bindigan waɗanda ƴan kasuwar suka ce kimanin mutum 50 ne, sun kai farmaki kasuwar ne da misalin ƙarfe 12:30 na rana a ranar Laraba, yayin da ake tsaka da gudanar da harkokin kasuwanci.

Ƴan bindigan suna isa suka toshe dukkanin hanyoyin shiga kasuwar, inda suka hana ƴan kasuwar tserewa.

Wasu daga cikin ƴan bindigan sun shiga kasuwar suna ƙwace kuɗi a hannun ƴan kasuwar, kafin daga bisani su yi awon gaba da kayayyaki ciki har da kayan abinci da yaduka.

Trust Radio ta tattaro cewa da yawa daga cikin ƴan kasuwar, waɗanda akasari sun fito ne daga ƙauyukan da ke kewaye da Jalingo, babban birnin jihar, ƴan bindigan sun sace su.

Kara karanta wannan

Yadda yan sanda suka cafke wata daliba mai ba yan bindiga bayanai, ta tona asiri

Mutanen yankin sun koka

Wani mazaunin garin mai suna Adamu Haruna ya ce ƴan bindigan sun yi harbi a iska domin tsorata ƴan kasuwar kafin su yi gargadin cewa duk wanda ya yi yunkurin fita daga kasuwar za su harbe shi.

Ya ce wannan ba shi ne karon farko da ƴan bindiga ke sace mutane a yankin ba, saboda a baya ƴan bindiga sun taɓa mamaye garin amma sojoji da mafarauta sun fatattake su.

Ba a iya samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba ba, saboda lokacin da aka kira shi wayarsa a kashe take.

Ƴan Bindiga Sun Ƙona Mata da Surukarta

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun ƙona wata mata tare da surukarta da ƴaƴanta biyu a wani hari a jihar Sokoto.

Ƴan bindigan sun kuma halaka wasu mutum 12 tare da yin awon gaba da wasu wasu matan aure a yayin harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng