Kano: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shari’ar Hafsat 'Chuchu' Da Ake Zargi da Kisan Kai, Ta Yi Bayani

Kano: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shari’ar Hafsat 'Chuchu' Da Ake Zargi da Kisan Kai, Ta Yi Bayani

  • Kotun Majistare ta umarci tsare matar aure da ake zargi da hallaka wani matashi mai suna Nafi’u Hafizu a jihar Kano
  • Kotun bayan karanto dukkan zarge-zargen ta tsare Hafsat tare da dage ci gaba da sauraren karar zuwa watan Faburairu
  • Ana zargin Hafsat da ke rayuwa a Unguwa Uku ana zarginta kan laifuka guda biyu da su ka hada da yunkurin kashe kai da kuma kisan kai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Kotun Majistare da ke jihar Kano ta umarci ci gaba da tsare Hafsat Surajo da aka fi sani da ‘Chuchu’ kan zargin kisa.

Wacce ake zargin an tsare ta ne bayan zargin ta hallaka Nafi’u Hafizu mai shekaru 38 har lahira a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: An tsare matashi a gidan kaso kan barazanar kawo karshen dattawan Unguwarsu, ya fadi dalili

Kotun Maistare ta umarci tsare matar aure da zargin kisan kai a Kano
Kotu ta umarci ci gaba da tsare Hafsat 'Chuchu' a gidan kaso. Hoto: @KanoPoliceNG.
Asali: Facebook

Mene ake zargin matar da aikata wa?

Hafsat da ke rayuwa a Unguwa Uku ana zarginta kan laifuka guda biyu da su ka hada da yunkurin kashe kai da kuma kisan kai, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Sahri’a, Hadiza Abdurahman ta umarci tsareta tare da dage shari’ar har zuwa ranar 1 ga watan Faburairu don ci gaba da sauraran karar.

Tun farko lauyan mai kara, Lamido Sorondinki ya fada wa kotun cewa Hafsat ta yi amfani da wuka mai kaifi don daba wa Nafi’u.

Ya ce ta daba masa wukar ce bayan ya yi kokarin hana ta kashe kanta wanda ya yi sanadin jiwa hannunta ciwo da wukar.

Mene martanin wacce ake zargin?

Wacce ake zargin a farko ta amincce da laifinta yayin da daga bisani ta musanta cewa ta aikata laifin da ake zarginta.

Kara karanta wannan

Kirsimeti: Yan Shi'a sun halarci bikin a coci, sun fadi kwararan dalilai masu kama hankali

Aikata wannan laifi ya sabawa sashin 281 da kuma 221 na kundin laifuka da hukunci, cewar Daily Post.

Har ila yau, mijin Hafsaf mai suna Dayyabu Abdullahi da kuma wasu mutum biyu, Adamu Muhammad da Nasidi Muhammad an tsare su da zargin hadin baki a laifin.

Soronkodi ya ce tun farko mijin matar ya yi karyar cewa Nafi’u ya rasu ne saboda rashin lafiyar da ke damunsa.

Yayin Dayyabu shi ma ya musanta aikata laifin da ake zarginsa a kai bayan aikata kisan da matarsa ta yi.

‘Yan sanda sun cafke matar da ta hallaka wani a Kano

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta cafke Hafsat Surajo da ake zargin ta hallaka matashi a Kano.

Rundunar kuma ta cafke mijinta da wasu mutane biyu kan zargin hadin baki wurin yin kisan kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.