Cikin Jimami an Binne Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Na'Abba, Manyan Najeriya Sun Halarta
- Daga karshe an binne marigayi Ghali Umar Na'Abba a jihar Kano da yammacin yau Laraba
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudden Abbas na daga cikin jiga-jigan da su ka halarci sallar jana'izar
- An dauki gawar marigayin zuwa Kano da misalin karfe 2 na rana zuwa gidansa don masa addu'o'i kafin wuce wa da ita kofar Sarki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - An binne tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba a jihar Kano.
Daga cikin manya-manyan baki da suka halarci jana'izar akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da kakakin Majalisar Wakilai, Tajudden Abbas.
Jiga-jigan da suka halarci jana'izar Na'Abba?
Sauran sun hada da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da Sanata Rabi'u Kwankwaso da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta tattaro cewa marigayin ya rasu a safiyar yau Laraba 27 ga watan Disamba a birnin Tarayya da ke Abuja.
An dauki gawar marigayin zuwa Kano da misalin karfe 2 na rana zuwa gidansa don masa addu'o'i kafin wuce wa da ita kofar Sarki.
Sallar jana'izar ta samu jagorancin Farfesa Sani Zaharadden da misalin karfe 5:38 na yamma.
Yaushe Na'Abba ya rasu?
Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da Sanata Kawu Sumaila duk sun sami halartar sallar jana'izar.
Da safiyar yau Laraba ce aka sanar da rasuwar Ghali Umar Na'Abba bayan ya sha fama a wani asibitin Abuja, cewar The Nation.
Jiga-jigan Najeriya da dama sun tura sakon jaje ga iyalan marigayin inda suka bayyana shi a matsayin mutum mai karimci.
Gwamna Abba Kabir ya kadu da rasuwar Na'Abba
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna alhinin rasuwar tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba.
Gwamnan ya bayyana Na'Abba a matsayin mutum mai kishin kasa wanda ya martaba dimukradiyya a rayuwarsa.
Har ila yau, Sanata Rabi'u Kwankwaso shi ma ana shi bangaren ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin.
Asali: Legit.ng