Sabani, Fada da Jerin Rigingimu 10 da Aka Yi da Rotimi Akeredolu Lokacin Rayuwarsa
- An fafata da Rotimi Akeredolu a lokacin yana mulki da sa’ilin da ya jagoranci kungiyar NBA a Najeriya
- Marigayin ne ya bada umarni makiyaya su bar jejin Ondo, wasu sun ce hakan ya sabawa dokar kasa
- Rotimi Akeredolu ya fito karara ya ce dole mulki ya bar Arewa, mutumin Kudu ya zama shugaba a 2023
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
A rahoton nan, za a ji irin gwagwarmayar da Rotimi Akeredolu ya yi a mulki
1. Rotimi Akeredolu ya lashe zaben 2016
An gwabza da Marigayi Rotimi Akeredolu wajen samun tikitin APC a 2016, bayan fadan gida, ya gwabza da Olusola Oke da Eyitayo Jegede.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Fatattakar makiyaya
A farkon shekarar 2021, Rotimi Akeredolu ya bada umarni duk wasu makiyaya da ke cikin jeji su bar jihar, wasu sun ce hakan ya saba doka.
3. Sai mulki ya koma Kudu
Gabanin zaben 2023, gwamnan Ondo yana cikin wadanda su kayi ta maganar dole sai mulki ya bar hannun ‘yan Arewa ya koma zuwa Kudu.
4. Shugaban gwamnonin Kudu maso yamma
Mai girma Rotimi Akeredolu ya jagoranci kungiyar gwamnonin jihohin Kudu maso yamma na Legas, Ekiti, Ondo, Osun, Ogun da Oyo a lokacinsa.
5. Amotekun
Marigayin yana cikin wadanda su ka yi uwa da makarbiya har aka kafa kungiyar Amotekun domin magance matsalar tsaro a Kudu maso yamma.
6. Sabanin Akeredolu da mataimakan gwamnonin Ondo
Kafin zaben 2023, Akeredolu ya samu sabani da mataimakinsa watau Agbola Ajayi. Bayan nan kuma haka ta sake faruwa da Lucky Ayedatiwa.
7. Yaki da tsarin kason mukamai a Majalisa
Daf da zai kwanta jinya, gwamna Akeredolu ya yaki jam’iyyarsa kan yadda ta ware kujerun shugabannin majalisa, ya zargi APC da rashin adalci.
8. Tazarcen Aketi a jam’iyyar APC
Da aka zo zaben tazarce a 2020, Marigayin ya yi galaba a kan Olusola Oke da irinsu Isaac Kekemeke da gagarumar nasara har zuwa babban zabe.
9. Sabani da manyan jam’iyya
Gwamna Akeredolu ya samu sabani da irinsu Sanata Ajayi Borrofice da Sanata Tayo Alasoadura a APC, har sun zarge shi da yakar Bola Tinubu.
10. Rotimi Akeredolu v Shugaba Ummaru ‘Yar’adua
Ana da labarin yadda a lokacin yana shugaban kungiyar lauyoyi na kasa (NBA), lauyan ya bukaci Ummaru Musa ‘Yar’adua saboda rashin lafiyarsa.
Asali: Legit.ng