Mutuwar Akeredolu: Shin Aiyedatiwa Ne Zai Zama Sabon Gwamnan Ondo? Ga Abin Da Doka Ta Ce
- Bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu, Lucky Aiyedatiwa, mataimakinsa na daf da zama sabon gwamnan jihar Ondo
- Wani lauya, Barista Oladotund Hassan, ya shaidawa Legit.ng cewa ya zama wajibi kamar yadda doka ta tanadar, a rantsar da mataimakin
- Kamar yadda aka sabunta, sashe na 191 1(1) na kundin tsarin mulkin 1999 shi ma ya tabbatar da wajabcin rantsar da mataimakin nan take
Jihar Ondo - Lucky Aiyedatiwa na shirin karbar mukamin gwamnan jihar Ondo biyo bayan samun labarin rasuwar gwamna Rotimi Akeredolu yana da shekaru 67 a duniya.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da rasuwar Akeredolu a Legas a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, inda ta bayyana cewa yanayin lafiyarsa ya hana a kai shi kasar waje neman magani.
Aiyedatiwa ya rike mukaddashin gwamna na mako biyu
Lafiyar Akeredolu ta kasance abin damuwa ga jama'a, bayan da ya dawo Najeriya a watan Satumba bayan hutun jinya na watanni uku a Jamus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwanan nan, ya mika mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, saboda lafiyarsa, The Cable ta ruwaito.
Bayan ya rike mukamin mukaddashin gwamna na kimanin makonni biyu, yanzu haka Aiyedatiwa na shirin zama gwamna bisa doka.
Abin da tsarin kundin mulkin 1999 ya ce game da halin da jihar Ondo ke ciki
Da yake karin haske game da wannan ci gaban, Barista Olatodun Hassan, sakataren kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) reshen Epe, ya shaidawa Legit cewa, abu ne da ya zama dole kuma a bisa doka ya kamata a rantsar da Aiyedatiwa cikin gaggawa.
Ya ce:
“Wannan dabi’a ce ta siyasa idan babu gwamna, mataimakin gwamna ya na daukar matakin gaggawa.
“Mahimmancin hakan shi ne tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin mulki ba tare da wata matsala ba, kuma bai kamata a zauna ba gwamna ba, kuma doka ce".
A halin yanzu, sashe na 191 1 (1) na kundin tsarin mulkin 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana cewa:
“Mataimakin gwamnan jiha zai rike mukamin gwamnan jihar idan ofishin gwamna ya zama babu kowa saboda mutuwa, ko murabus, ko tsige shi, rashin iya aiki na dindindin.
"Ko kuma a tsige gwamna daga mukaminsa saboda wani dalili na daban bisa ga sashe na 188 ko 189 na wannan dokar."
An fara shirin rantsar da sabon gwamnan Ondo
Jim kadan bayan sanar da mutuwar Akeredolu, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wani jigo a jam'iyyar APC ya sanar da cewa an fara shirin rantsar da sabon gwamnan jihar Ondo.
A cewar jigon jam'iyyar, za a rantsar da mataimakin gwamnan na yanzu, Lucky Aiyedetiwa matsayin sabon gwamna don ci gaba da jan ragamar mulkin jihar.
Asali: Legit.ng