Na’Abba: Kwankwaso, Abba Kabir Sun Kadu Kan Rasuwar Tsohon Kakakin Majalisa, Sun Tura Muhimmin Sako

Na’Abba: Kwankwaso, Abba Kabir Sun Kadu Kan Rasuwar Tsohon Kakakin Majalisa, Sun Tura Muhimmin Sako

  • Jigon jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna alhinin rasuwar tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba
  • Kwankwaso ya jajantawa iyalan marigayin da gwamnatin jihar Kano kan rasuwar inda ya ce tabbas an yi babban rashin mutumin kirki
  • Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Laraba 27 ga watan Disamba inda ya masa addu’ar samun rahama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir sun jajantawa iyalan marigayi Ghali Umar Na’Abba kan rasuwarshi.

Kwankwaso ya nuna alhininsa kan rasuwar inda ya ce tabbas an yi babban rashin mutumin kirki.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi ta'aziyyar Ghali Na'abba, ya bayyana muhimmin abu 1 da ya yi domin ceto Najeriya

Kwankwaso ya tura muhimmin sako kan rasuwar tsohon kakakin Majalisar Wakilai
Kwankwaso ya nuna alhini kan rasuwar Ghali Umar Na'Abba. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Facebook

Mene Kwankwaso ya ce kan rasuwar Na'Abba?

Jagoran siyasar Kano ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Laraba 27 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Na’Abba ya tsaya tsayin daka kan bin ka’ida da kuma tabbatar da ganin an samar da tsari a rayuwar ‘yan kasar.

Sanatan ya kuma yi addu’ar samun rahama ga mamacin inda a tura sakon jaje ga iyalansa da kuma gwamnatin jihar Kano.

Wace addu'ar Kwankwaso ya yi?

Ya ce:

“Innalillah wa inna ilaihi rajiun, cikin alhini da mika komai ga Ubangiji na samu labarin rasuwar tsohon Kakakin Majalisa, Ghali Umar Na’Abba.
“Hon. Na’Abba ya kasance mai dogewa kan ra’ayinsa kuma mai bin ka’idoji da tabbatar da samar da tsari a rayuwa.
“Muna addu’ar Allah madaukakin Sarki ya biya shi da gidan aljanna Firdausi, ina mika sakon jaje ga iyalansa da mutanen Kano da kuma gwamnatin jihar.”

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 5 muhimmai da ya kamata Ku sani game da marigayi Ghali Umar Na'Abba

Mene Abba Kabir ke cewa?

A martaninshi, Gwamna Abba Kabir ya jajantawa iyalan marigayi Ghali Umar Na'Abba inda ya ce an tafka babban rashi.

Abba ya ce marigayin mutum ne da ya tsaya tsayin daka don tabbatar da dimukradiyya da bin doka.

Ya jajantawa iyalansa da Majalisar Wakilai da sauran 'yan siyasa da sauran al'ummar jihar Kano.

Umar Na’Abba ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, an wayi garin yau Laraba da mummunan labarin rasuwar tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba.

Marigayin ya rasu ne a yau Laraba 27 ga watan Disamba a wani asibiti da ke birnin Taraya Najeiya, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.