Yan BindIga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Bayin Allah a Wani Yanayi Mara Dadi
- An shiga jimami a jihar Sokoto bayan ƴan bindiga sun tafka ta'asa a wani mummunan hari da suka kai a jihar Sokoto
- Miyagun ƴan bindigan a yayin harin sun ƙona wata mata da surukurarta da ƴaƴanta biyu a ƙaramsar hukumar Rabah
- Ƴan bindigan sun kuma halaka wasu mutum 12 da sace wasu mata uku a harin da suka kai a daren ranar Lahadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Wasu miyagu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun ƙona wata mata da surukarta da kuma ƴaƴanta biyu da ransu a wani harin da suka kai a jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Kurya da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun kashe mutanen ƙauyen 12 tare da sace mata uku a yayin harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin yankin, Yusuf Garba ya ce ɗaya daga cikin wadanda aka sace ta rasa mijinta a harin, rahoton Trust Radio ya tabbatar.
"Daga cikin wadanda aka kashe akwai wata mace ɗaya da aka ƙona ta mutu tare da surukarta da ƴaƴanta biyu a cikin ɗakinsu." A cewarsa.
A cewarsa, daga baya maharan sun yi wani ƙazamin faɗa da sojoji.
"Muna zargin su ma sun yi asara mai yawa saboda mun ga tabon jini a inda suka ajiye babura. Amma ka san ba sa barin gawarwakinsu a baya." A cewarsa.
Me ƴanda suka ce kan lamarin?
Sai dai rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai ne a yayin harin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i, ya ƙara da cewa suna cigaba da tattara alƙaluman waɗanda suka mutu.
Ƴan Bindiga Sun Halaka Ƴan Kasuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan wasu ƴan kasuwa a jihar Katsina.
Ƴan bindigan a yayin farmakin sun halaka mutum shida har lahira tare da raunata wasu mutum huɗu tare da yin awon gaba da wasu mutum biyu.
Asali: Legit.ng