Murna Yayin da Gwamnatin Tarayya Ta Fara Rabawa Talakawa N20,000
- Gwamnatin tarayya ta fara rabawa marasa galihu kudi N20,000 a jihar Cross River
- Ministan jin kai da kawar da talauci, Dokta Betta Edu, ta ce Shugaban kasa Tinubu ya jajirce don rage talauci a kasar
- Edu ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta kaddamar da shirin kawo kashen Yunwa da koyar da mutane aikin hannu a watan Janairun 2024
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Cross River, Calabar - Gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta fara rabawa marasa gata kudi N20,000 a jihar Cross River.
Shirin wanda ya gudana a ranar Litinin, 25 ga watan Disamba yana daga cikin kokarin da ake yi na kawo karshen talauci a kasar.
Gwamna Bassey Otu wanda ya samu rakiyar ministan jin kai da kawar da talauci, Dr Betta Edu ne ya kaddamar da shirin a Calabar., rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Edu yace shugaba Tinubu ya kuduri aniyar rage radadin talauci.
Ministar ta ce:
“Gwamnatin tarayya ta samar da shirye-shirye da dama kamar su Kudin Manoma, Kudin yan kasuwa, raba kudi, wanda yan Najeriya miliyan 3.5 suka ci gajiyar su a fadin hukumar.
“Muna kuma da shirin kawo karshen yunwa da za a kaddamar a watan Janairu, da kuma shirin koyar da sana'o; da sauransu, abun da nake bukata kawai a matakin jiha shine jihar ta bayar da cikakken goyon baya."
Otu yace shugaba Tinubu na bukatar hadin kan ‘yan Najeriya domin samun nasara a aikin fitar da mutane miliyan 50 daga kangin talauci nan da 2030.
Ma'aikata sun yi Kirsimeti ba albashi
A wani labarin, mun ji cewa galibi ba'a yi bikin Kirsimeti cikin jin dadi ba kamar yadda aka saba a gidan ma'aikatan gwamnatin tarayya da dama, inda aka samu karancin dafe-dafen abinci da ziyarce-ziyarce saboda tsaiko da aka samu wajen biyan albashin watan Disamban 2023.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, ma'aikata da ke aiki a hukumomin tattara kudaden shiga kamar su NNPC, NPA, NIMASA, NCC, CBN, da FIRS ne kadai suka samu albashinsu na Disamba.
Asali: Legit.ng