Ana Cikin Bikin Kirsmeti Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutum 6

Ana Cikin Bikin Kirsmeti Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutum 6

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan wasu ƴan kasuwa a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina
  • A yayin harin ƴan bindigan sun halaka mutum shida tare da raunata wasu mutum huɗu da sace wasu mutum biyu
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar harin inda ya ce tuni ƴan sanda sun bi sahun miyagun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Masu makoki a ranar Kirsimeti sun binne wasu ƴan kasuwa guda shida da ƴan ta’adda suka kashe a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Mazauna yankin sun bayyana cewa an kashe ƴan kasuwar ne da yammacin ranar Lahadi a lokacin da suke dawowa daga kasuwar Jibia zuwa ƙauyen Yan Gayya da ke ƙaramar hukumar, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe ƴan kasuwa takwas, sun tafka mummunar ɓarna a jihar arewa

Yan bindiga sun halaka yan kasuwa a Katsina
Yan bindiga sun halaka yan kasuwa a wani hari a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Mazauna yankin sun bayyana ƴan kasuwar da aka kashe sun haɗa da, Yusuf Karamiusu, Sale Lamin, Dan Hameme, Mallam Shafi, Mallam Dikke da Kashim Samiu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun ce an binne su ne a ranar Litinin a ƙauyen Yan Gayya, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ƴan bindigan sun tafka ɓarna

Mazauna yankin sun kuma bayyana cewa wasu mutum huɗu da suka haɗa da Biliyaminu, Mallam Jafaru, Lawal Dachi da kuma Dan Hasuma sun samu raunuka a harin, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Mazauna yankin sun ƙara da cewa a halin yanzu dukkan mutanen huɗu suna jinya a asibiti. Ƴa ta'addan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane biyu a yayin harin waɗanda suka haɗa da Alhaji Abdurashidi da Abdu Teacher.

Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan ta’addan waɗanda ake kyautata zaton suna guduwa ne daga hare-haren da jami’an tsaro ke kai musu a jihar Zamfara, sun harbe motar da ƴan kasuwar ke tafiya a ƙauyen Kukar Babangida.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka halaka babban likita a yanayi mara dadi a gaban iyalansa

An bayyana cewa da farko ƴan ta’addan sun harbe direban motar har lahira inda suka tilasta wa motar tsayawa.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, Abubakar Aliyu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kuma ƙara da cewa tuni jami’an tsaro suka fara farautar ƴan ta’addan.

"Eh, gaskiya ne. Rundunar ƴan sandan ta tura jam'ianta domin zaƙulo waɗanda suka aikata laifin." A cewarsa.

Ƴan Bindiga Sun Tafka Ɓarna a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan hari a wasu ƙauyukan jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun halaka mutum 145 a ƙauyuka 23 na ƙananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng