Gwamna Dauda Zai Kashe Naira Biliyan 1.95 Don Sake Gina Fadar Sarakunan Gargajiya a Zamfara

Gwamna Dauda Zai Kashe Naira Biliyan 1.95 Don Sake Gina Fadar Sarakunan Gargajiya a Zamfara

  • Akalla naira biliyan 1.95 gwamnatin jihar Zamfara ta ware don sake gina fadar sarakuna 18 a jihar, da nufin daga darajar sarakunan gargajiya
  • Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Ahmad Yandi ya ce an ware kudin ne daga kasafin jihar na 2024
  • Idan ba a manta ba Gwamna Dauda Lawal na jihar ya gabatarwa majalisar dokokin jihar naira biliyan 423.5 matsayin kasafin kudin 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1.95 daga kasafin 2024 don sake gina gidajen sarakuna 18 da ke a fadin jihar.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Ahmad Yandi, ya bayyana hakan a ranar Litinin a Gusau.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya amince da rabawa ma'aikatan jiharsa kudi mai tsoka don bikin Kirsimeti

Gwamnatin Zamfara za ta gina fadar sarakuna 18
Gwamna Daudawa zai kashe naira biliyan 1.95 don sake gina fadar sarakunan gargajiya a Zamfara Hoto: @ZamfaraGovernor
Asali: Twitter

Dalilin sake gina fadar sarakuna a Zamfara - Yandi

Yandi wanda ya bayyana gaban kwamitin kudi da kasafi na majalisar jihar ya ce aikin ginin zai daga darajar sarakunan gargajiya, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Dauda Lawal ya gabatar da naira biliyan 423.5 matsayin kasafin kudin 2024 gaban majalisar dokokin jihar don amince wa.

Yandi wanda ya bayyana gaban kwamitin don kare kasafin ma'aikatarsa, ya ce na daga cikin yunkurin gwanati na daga darajar masarautun gargajiya a jihar.

Abubuwan da kasafin 2024 na jihar Zamfara ya kunsa

A nashi bangaren, babban sakataren ma'aikatar ayyuka da gine-gine, Alhaji Shehu Baraya ya ce an ware naira biliyan 140 don aikin tituna da wasu ayyukan a jihar, rahoton Leadership.

Shi ma kwamishinan gidaje da bunkasa karkara, Alhaji Kabiru Moyi, ya ce akwai shirin gwamnati na gina wani birni a wajen garin gusau don bunkasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya ware naira biliyan 15.97 don yin wasu manyan ayyuka 2 a kwaryar jihar Kano

Kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito Moyi na cewa an ware akalla naira biliyan 10 don gina wannan birnin wanda aka yi wa taken 'economic city'.

Watan Janairu 2024 Tinubu zai saki sunayen wadanda zai ba tallafin N50k

A wani labarin, Betta Edu, ministar jin kai da kawar da fatara ta yi alkawarin wallafa sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin shugaban kasa na naira dubu hamsin.

Bettu Edu ta tabbatar da sakin sunan a watan Janairu a wata hira da Channels TV’s a ranar Juma'a inda ta ce shirin zai rage radadin cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.