Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Tsohon Ciyaman da Wasu 10 a Jihar Arewa
- Yan bindiga sun farmaki al'ummar Dila da Kunini a kananan hukumomin Lau da Yorro da ke jihar Taraba a ranar Lahadi, 24 ga watan Disamba
- Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da tsohon ciyaman na karamar hukumar Yorro, Hon. Ishaya Dimas Dila
- Haka kuma, maharan sun tisa keyar wasu mutum 10 zuwa cikin jeji bayan sun harbi wasu biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da tsohon ciyaman na karamar hukumar Yorro, Hon. Ishaya Dimas Dila, tare da wasu mutum 10 a kauyen Dila da Kunini, a ranar Lahadi.
An tattaro cewa maharan sun sace tsohon ciyaman din da wasu mutum biyu a kauyen Dila da ke karamar hukumar Yorro ta jihar Taraba a safiyar ranar Lahadi.
Yadda yan bindiga suka farmaki al'ummar Taraba tare da sace mutane
Haka kuma, yan bindiga sun harbi mutum biyu a kauyen Kunini da ke karamar hukumar Lau a wannan rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an harbi mutum biyun ne yayin da suka nunawa masu garkuwa da mutanen turjiya a yayin sace su.
An kuma tattaro cewa maharan sun yi awon gaba da mutum takwas a kauyen Kunini yayin harin.
Bincike ya nuna cewa cikin kwanaki 10 da suka gabata, mutum 40 aka sace a Dila, Pupule, Maraban Kunini da kauyen Kunini a kananan hukumomin Lau da Yorro da ke jihar.
Martanin yan sanda
Da yake tabbatar da lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar al'amarin.
Abdullahi ya ce tuni jami'an yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro suka fara bi sahun masu garkuwa da mutanen, rahoton Daily Post.
Ya jad dada jajircewarrundunar na ganin an ceto duk wadanda aka yi garkuwa da su a fadin jihar ba tare da sun ji rauni ba.
Yan bindiga sun farmaki al'ummar Katsina
A wani labarin kuma, mun ji cewa yan ta’adda sun kashe wasu ‘yan kasuwa 8 da ke dawowa daga kasuwar mako-mako ta Jibia a kusa da kauyen Kukar Babangida da ke Jihar Katsina.
An rahoto cewa yan kasuwan sun rasa rayukansu ne yayin da 'yan bindigan suka buɗe wa motar da suke ciki wuta ranar Lahadi, 24 ga watan Disamba, 2023.
Maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutum biyu kana suka jikkata ƙarin wasu fasinjoji huɗu da ke cikin motar.
Asali: Legit.ng