'Yan Bindiga Sun Kashe Yan Kasuwa Takwas, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Jihar Arewa
- 'Yan bindiga sun halaka ƴan kasuwa takwas da ke kan hanyar dawowa daga kasuwar mako-mako a Jibia, jihar Katsina
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa motar da yan kasuwan ke ciki wuta, suka raunata wasu mutum huɗu
- Hukumar yan sanda ta bayyana cewa ta ɗauki matakan kare kai harin a gaba da kuma kamo waɗanda suka aikata ɗanyen aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - ‘Yan ta’adda sun kashe wasu ‘yan kasuwa 8 da ke dawowa daga kasuwar mako-mako ta Jibia a kusa da kauyen Kukar Babangida da ke Jihar Katsina.
Premium Times ta ce ƴan kasuwan sun rasa rayukansu ne yayin da 'yan bindigan suka buɗe wa motar da suke ciki wuta ranar Lahadi, 24 ga watan Disamba, 2023.
Maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutum biyu kana suka jikkata ƙarin wasu fasinjoji huɗu da ke cikin motar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanda suka samu raunuka a harin, Bilyaminu, Malam Jafaru, Lawal Dadi da kuma Dan Husuma, suna kwance a wani asibiti ana kula da lafiyarsu.
An tattaro cewa ƴan ta'addan da suka aikata wannan ɗanyen aikin sun gudo ne daga luguden wutan rundunar sojin saman Najeriya a yankin Zurmi, jihar Zamfara.
An bayyana sunayen wadanda aka kashe, Sani Na Gogara, Yusuf Karamin su, Sale Lami, Dan Hameme, Malam Shafi’i, Malam Dikke da Bashir Sani, duk an masu jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da harin
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin ƴan sandan ya ce:
"Eh gaskiya ne amma tunu rundunar ƴan sanda ta ɗauki matakan kate afkuwar haka nan gaba kuma ta baza komarta ko ina da nufin kamo waɗanda suka kai harin."
"Kwamishinan ƴan sanda ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukan su sakamakon wannan hari."
Ya ce a ƴan makonnin da suka gabata an samu raguwar hare-haren ƴka ta'adda a Katsina saboda irin matakan da gwamnatin jiha da ta tarayya suka dauka.
Wani mazaunin Jibia, Abdullahi Gambo, ya shaida wa Legit Hausa cewa mutum ɗaya daga cikin waɗanda suka jikkata ya rasu, jimulla an kashe mutane 9 kenan.
Da yake tabbatar mana da harin, mutumin ya ce:
"Yan bindiga sun mamaye su ne kuma suka buɗe musu wuta, mutum takwas suka mutu, daga baya ɗaya daga cikin mutum huɗu da suka ji rauni rai ya yi halinsa."
"Lamarin babu daɗi amma duk da haka zamu ce an samu saukin matsalar tsaro a Katsina, gwamnati na iya bakin kokarinta amma ba zaka ce ga lokacin da ƴan ta'addan nan zasu fito ba."
An kashe mutane 16 a Filato
A wani rahoton na daban Mutanen da ba su gaza 16 sun rasa rayukansu a wani sabon harin ƴan ta'adda a kauyen Mushu da ke jihar Filato.
Rundunar sojin haɗin guiwa ta Operation Save Haven ta tabbatar da kai harin ranar Asabar kuma ta ɗauki mataki.
Asali: Legit.ng