Kirsimeti: Sanatar Arewa Ta Raba Wa 'Yan Mazabarta Tirelar Shinkafa 6 da Sauran Kaya, Ta Yi Gargadi

Kirsimeti: Sanatar Arewa Ta Raba Wa 'Yan Mazabarta Tirelar Shinkafa 6 da Sauran Kaya, Ta Yi Gargadi

  • Yayin da ke cikin bukukuwan Kirsimeti a Najeriya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gwangwaje 'yan mazabarta
  • Natasha da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta raba tirelar shinkafa shida da litattafai dubu 20 da kuma zannuwa dubu 10
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hidiminta a bangaren yada labarai, Arogbonlo Israel ya fitar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gwangwaje 'yan mazabarta da abin alkairi yayin bikin Kirsimeti.

Sanatar da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta raba tirelar shinkafa shida da litattafai dubu 20 da kuma zannuwa dubu 10, Legit ta tattaro.

Sanatar Arewa ta gwangwaje 'yan mazabarta da abin arziki yayin bikin Kirsimeti
Sanata Natasha ta raba tirelar shinkafa 6 don bikin Kirsimeti. Hoto: Natasha Akpoti-Uduaghan.
Asali: Twitter

Ta yaya za a raba kayayyakin da Natasha ta bayar?

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta fara tuhumar wasu manyan ministocin Buhari kan badakalar naira biliyan 187

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da hidiminta a bangaren yada labarai, Arogbonlo Israel ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Israel ya ce Sanatar ya kuma raba jakukkunan yaran makaranta guda dubu biyar a mazabar ta Kogi ta Tsakiya.

Sanarwar ta ce kayayyakin ba iya 'yan jami'yyar PDP ne kadai za su amfana ba, kowa ma ya shafe shi.

Har ila yau, rahotanni sun tabbatar da cewa za a raba dukkan kayan ne a kananan hukumomi biyar da ke mazabar ta Kogi ta Tsakiya.

Mene dalilin ba da tallafin da Natasha ta bayar?

Kananan hukumomin sun hada da Adavi da Ajaokuta da Okene da Okehi da kuma Ogori-Mangogo da ke jihar.

Natasha ta ce bikin Kirsimeti lokaci ne na nuna kauna da kuma taimakon mutane musamman marasa karfi a cikin al'umma.

Ta bayyana amfanin raba kayayyakin ga jama'a musamman marasa karfi don samun gudanar da bikin cikin annashuwa.

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

Bello ya raba motocin alfarma ga 'yan Majalisa, Alkalai

A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya raba motocin alfarma 44 ga 'yan Majalisa a jihar da alkalai.

Bello ya kuma raba wasu motocin daukar marasa lafiya 25 ga kananan hukumomi a jihar don taimakawa marasa lafiya.

Gwamnan ya ce ya yi hakan don saka musu da irin bautar da suke yi a jihar ba dare ba rana don ganin ci gaban jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.