CBN: Babu Kanshin Gaskiya a Zargin da Ake Yi Mani – Godwin Emefiele Ya Dauki Mataki
- Godwin Emefiele ya karyata rahoton da ake yadawa game da binciken abubuwan da su ka faru a bankin CBN
- Tsohon gwamnan babban bankin ya tabbatar da cewa Muhammadu Buhari ya amince da canjin takardun kudi
- Jawabin Emefiele ya zargi kwamitin Jim Obazeee da sharri saboda a bata masa suna a wajen mutanen Najeriya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Godwin Emefiele ya musanya zargin da ake yi masa na tafka barna a lokacin da yake rike da babban banki kasa na CBN.
Godwin Emefiele ya yi watsi da rahoton binciken da Jim Obazee ya yi a wani jawabi da ya fitar, Punch ta tabbatar da wannan labari.
Godwin Emefiele ya ce an yi masa sharri
Mista Godwin Emefiele ya saki jawabin ne a yammacin Lahadi, ya karyata zargin boye kudi a wasu bankuna da ke kasashen waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin da ya yi, Emefiele ya ce rahoton ba komai ba ne sai yunkurin bata sunan shi, ci masa mutunci saboda son ran mai binciken.
Ganin halin da yake ciki, tsohon gwamnan ya ce an ba shi shawarar ya yi shiru, lauyoyinsa za su dauki matakin da ya dace a kotu.
Duk da haka, Emefiele ya ce dole ya yi magana a game da wasu zargin da aka jefe shi da su, wanda ya ce sam ba su da alaka da gaskiya.
Rahoton ya yi ikirarin an cire $6.23m daga asusun CBN a kan umarnin bogi da sa hannun Muhammadu Buhari GCFR da Boss Mustapha.
"Makonni biyu da su ka wuce, a gaban lauyoyi na, Jim Obazee da wani Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda daga CID sun zo Kuje domin yi mani tambayi a kan takardun da ake magana.
Na fada masa ban san da wannan umarni daga tsohon shugaban kasa da tsohon SGF. Na fada masa ban taba jin maganar takardun ba."
- Godwin Emefiele
Emefiele, Buhari da canjin kudi
An rahoto tsohon gwamnan bankin CBN yana cewa shugaban kasa ya amince da canjin kudi da aka yi, kuma Jimi Obazee ya san haka.
A lokuta da-dama, Emefiele ya ce Mai girma Muhammadu Buhari GCFR ya shaidawa duniya ya yi na’am da canjin Nairori da CBN ya yi a 2022.
Asali: Legit.ng