Ba Dani Ba: Sheikh Dahiru Ya Yi Martani Kan Wasikar da Aka Ce Ya Rubuta Kan Rikicin Abba da Gawuna
- Sheikh Dahiru Bauchi ya yi watsi da wata wasikar da ake yadawa, inda aka ce malamin ya tura sako ga jojin kasa
- Dan Shehi ya ce sam ba daga mahaifinsa ta fito ba, ya yi karin haske game da wannan wasikar da ta yadu
- Ana ci gaba da jiran tsammani kan hukuncin da kotu za ta yanke a kwanan nan a shari'ar Abba da Gawuna
Jihar Bauchi - Fitaccen malamin addini a jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman-Bauchi, ya musanta cewa yana da alaka da wata wasika da ke yawo a kafafen sada zumunta mai magana kan batun shari'ar zaben gwamnan Kano.
A cikin wasikar aka ce Shehi ya aika wa babban jojin Najeriya (CJN) Olukayode Ariwoola, malamin ya yi kira ga mai shari’a da ya tabbatar da cewa kotun koli ta yi hukunci a shari'ar da gaskiya, amana da adalci.
"Kada ka tsoma baki a kitimurmurar da ke tsakanin Abba da Gawuna a Kano", Dattijan Yarbawa ga Tinubu
A baya an ruwaito yadda hotun koli ta tanadi hukuncin da za ta yanke a karar da aka shigar gabanta na Gwamnan Kano a ranar Alhamis din da ta gabata.
Yadda batun ya faro a farko
Kotun kolin ta tanadi hukuncin ne bayan sauraron bangarorin da suka daukaka kara, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan da kotun koli ta alanta cewa, ta tanadi hukuncin da za ta yanke a shari'ar tsakanin Abba da Gawuna.
Sai dai a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi, mataimakin shugaban gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sayyadi Tijjani, wanda kuma daya ne daga cikin ‘ya’yan malamin, ya yi watsi da wasikar.
Da yake magana a madadin mahaifinsa, ya ce takardar ta bogi ce kuma ba ta fito daga gare shi ba ko da wasa.
Bayani daga fadar Shehi
Ya ce:
“Hankalin mu ya kai ga wasikar da aka ce an aike wa babban jojin Najeriya. Jama'a daga bangarori daban-daban na ta kira da a tabbatar da kuma tantance sahihanci da gaskiyar wasikar.
“Gaskiyar magana ita ce wasikar ba ta fito daga wajen Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba. Tambarinta ba irin wanda Sheikh Dahiru Bauchi ke amfani da ita bace."
Hakazalika, ya tsokaci da cewa, Shehi kan yi amfani da hatimi a karshen kowacce wasika da rubuta, Daily Post ta tattaro.
Rade-radin da ake yadawa
A tun farko, rade-radi yana yawo cewa Dahiru Usman Bauchi ya rubuta takarda zuwa ga Alkalin Alkalan Najeriya a game da shari’ar zaben Kano.
Rahotannin da ke yawo sun ce Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya tsoma baki a kan shari’ar zaben gwamnan jihar Kano da ke gaban kotun koli.
Asali: Legit.ng