Dan Sanda Ya Bindige Jarumin Fina-Finan Najeriya, Azeez, Bisa Kuskure
- Ƴan wasan kwaikwayo a masana’antar fina-finan Najeriya sun yi koka bayan da wani ɗan sanda ya harbe wani abokin aikinsu
- Mutumin da aka fi sani da Azeez Ijadunade jarumi ne kuma daraktan fina-finai wanda aka harbe shi a Iperu a jihar Ogun
- Abokin aikinsa, Biodun Adebanjo ne ya wallafa abin baƙin cikin a shafinsa na Instagram inda ya ce an kai Ijadunade asibiti
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ogun - Wani ɗan sanda ya harbi fitaccen jarumin fina-finan Najeriya kuma mai shirya fina-finai, Azeez Ololade Ijaduade, a garin Iperu na jihar Ogun.
A halin yanzu yana kwance rai a hannun Allah a Asibitin Koyarwa na jami'ar Babcock da ke Ilishan Remo, cewar rahoton jaridar The Punch.
Hakan dai ya bayyana ne a wani saƙon da abokin aikin Ijaduade, Abiodun Adebanjo, ya sanya a shafinsa na Instagram mai suna @iamabiodunadebanjo, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya rubuta cewa:
"Don Allah muna buƙatar taimako a Iperu. Wani jami’in ƴan sandan Najeriya ya harbe darakta na, Azeez Ijaduade, @kingzeez1.
"A halin yanzu yana Asibitin Koyarwa na jami'ar Babcock. Duk wanda ke da lambar IG ko kwamishinan ƴan sanda ya taimaka mana."
Har yanzu dai babu cikakken ƙarin bayani game da lamarin saboda saƙon da Lehit Hausa ta aikewa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, a safiyar ranar Lahadi ba ta dawo da amsar sa ba.
Jarumin Fim ya rasu
A baya labari ya zo cewa shahararren jarumi a masana'antar shirya fina-finan turanci, Nollywood da ke kudancin Najeriya, Dejumo Lewis, ya riga mu gidan gaskiya.
Fitaccen jarumin ya rasu ne yana da shekaru 80 a duniya bayan fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana ta ba.
Shan Barasa Ya Kusa Halaka Jarumin Fim
A wani labarin kuma, kun ji cewa Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood Pete Edochie, ya bayyana yadda shan barasa ya kusa aika shi lahira.
Jarumin ya bayyana cewa akwai wata rana da ya kusa gamuwa da ajalinsa bagan ya kwankwaɗi barasa sannan ya kama tuƙin mota.
Asali: Legit.ng