"Na Yi Iya Bakin Kokarina a Matsayin Shugaban Kasar Najeriya", Ibrahim Babangida
- Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida ya shawarci matasan Najeriya wadanda sune shugabannin gobe
- IBB ya bukaci matasan da su karanci kasar da kyau, sannan su fahimci mutanen cikinta don ta haka ne kawai za su cimma nasara yayin shugabanci
- Ya kuma jadadda cewar ya yi iya bakin kokarinsa a lokacin da yake matsayin shugaba a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Minna, Jihar Niger - Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya bayyana cewa babban nasarar da ya samu a matsayin jagoran Najeriya shine sanin kasar sosai da kuma yin abokai a fadin ko'ina.
Ya bayyana a wata hira ta musamman da gidan radiyo na jami'ar FUT Minna cewa zai shawarci matasan Najeriya da ke neman takarar shugabancin kasar da su nemi sanin mutanen ciki da fahimtar Najeriya sosai.
Da aka bukaci ya kimanta nasarorin da ya samu a iya rayuwarsa, tsohon shugaban kasar ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na farko shine na bautawa kasar iya yadda zan iya, ba lallai ya gamsar da ku ba amma na yi iyakar abin da zan iya; na barwa tarihi ya yanke hukunci kan haka.
“Na yi hulda mai kyau da mutanen kasar. Ba ni da wata matsala da su kuma na kara sanin kasar sosai kasancewar ina tafiya sosai. Na yi abokai a duk fadin kasar kuma na yi tunanin hakan na daya daga cikin manyan nasarorin da nasamu."
IBB ya yi kira ga matasan Najeriya
IBB kamar yadda ake yi masa inkiya ya ce ya kamata matasan Najeriya su yi kokarin sani da fahimtar kasar saboda sune za su jagoranci kasar a nan gaba, rahoton Leadership.
Ya ce:
"Kuna da dama a yanzu a matsayinku na matasa, ku nemi sanin kasar, ku karanci kasar, mutanenta kuma idan kuka yi naarar yin haka ko fahimtar haka, ina tunanin hakan zai taimaka sosai wajen shirya ku ga shugabancin kasar."
Kan tsarin shugabancinsa, ya kara da cewar:
"Kamar dai kowani tsari, an daura ka a mukami na shugabanci, aikinka shine jagorantar mutane. Ka hau mizanin da mutane ke duba gareka don magance wasu matsalolinsu ko tsoronsu.
"Koma menene kuma kana nan a matsayin wanda zai yi haka. Don haka dole ne ka karanci mutane, dole ka dunga karatu a kansu kuma dole ka zamo mai tausayi. Wasu lokutan mara tausayi don yin abubuwa yadda ya kamata amma akwai hanyoyi da yawa da ya zama dole ka bunkasa saboda ka iya cimma wasu abubuwa. Wasu kuma ka roke su, wasu ka tursasa su da sauransu.”
Dangane da yakin basasa, Janar Babangida ya ce abin bakin ciki ne kuma ba zai so a sake yin irin hakan ba — wato fada da wadanda kuka horar da su domin hadin kan kasa.
Fasto Ayodele ya yi hasashe kan 2024
A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele, ya bayyana hasashensa game da 2024, kamar yadda yake bisa al'adar malaman addini a kasar.
Hasashen nasa wanda ke kunshe da shafuka 91, dauke da sa hannun hadiminsa, Osho Oluwatosin, malamin ya jaddada bukatar yin addu'a sosai don farfado da tattalin arzikin Najeriya a shekara mai zuwa.
Asali: Legit.ng