Kwalejin Kimiyya Ta Nasarawa Ta Dauki Tsatsauran Mataki Kan Dalibai Mata 7, Cikakken Bayani

Kwalejin Kimiyya Ta Nasarawa Ta Dauki Tsatsauran Mataki Kan Dalibai Mata 7, Cikakken Bayani

  • An dakatar da wasu dalibai 7 na kwalejin kimiyya ta Isah Mustapha Agwai da ke jihar Nasarawa kan yada hotunan rashin tarbiyya yayin bikin yaye dalibai
  • An bukaci daliban da abin ya shafa da su gabatar da wasikun rantsuwa daga waliyyansu, tare da tabbacin nuna kyawawan dabi'u idan suka dawo
  • Kamar yadda kwamitin makarantar ya yanke, za a sokewa daliban mata su bakwai zangon karatu daya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A wani mataki na tabbatar da ingancinta, kwalejin kimiyya ta Isah Mustapha Agwai (IMAP) da ke jihar Nasarawa ta dakatar da wasu dalibai bakwai da suka wallafa hotunan rashin tarbiya a shafukan sada zumunta yayin bikin yaye dalibai.

Wannan hukunci na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na makarantar, Mista Ali Hassan Mohammed ya fitar, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya amince da rabawa ma'aikatan jiharsa kudi mai tsoka don bikin Kirsimeti

Daliban wata makarantar gaba da sakandare
An yi amfani da hoton don misali ne mutanen basu da alaka da labarin Hoto: Frédéric Soltan/Getty Images
Asali: Getty Images

Daliban da abun ya shafa, gaba dayansu mata, sun yi asarar zangon karatu daya kuma an bukaci su gabatar da wasikun rantsuwa daga magabatansu, tare da tabbatar da kyawawan dabi'u idan suka dawo a zangon karatu na 2023/2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwalejin kimiyya ta Isah Mustapha Agwai (IMAP), jihar Nasarawa, ta amince da dakatar da sun ne yayin taronta na ranar 4 ga watan Oktoba 2023, tana mai nuni ga wallafa hotunan rashin tarbiya da daliban suka yi tare da bata sunan makarantar.

A halin da ake ciki, shugabar kwalejin, Dr Justina Anjiode Kotso, ta gargadi daukacin daliban da su guji duk wani nau’i na munanan dabi’u da kuma duk wani abu da zai iya jefa su cikin matsala, tare da cewa ba za su yarda a bata masu suna da nagarta ba.

Yan bindiga sun sace malamar jami'a

Kara karanta wannan

“Na kashe shi ne saboda ya hana ni kashe kaina”: Matar da ake zargi da kashe abokin mijinta a Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu mahara ɗauke da muggan makamai a daren ranar Lahadi, sun yi awon gaba da wata malamar jami'a ta jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi, Dakta Comfort Adokwe, cewar rahoton Daily Trust.

Jaridar The Punch ta ce ƴan bindigan sun kai farmaki gidanta ne da ke Angwan Jaba a cikin ƙaramar hukumar Keffi, inda suka yi awon gaba da ita yayin da suke ta harbe-harben bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng