Gwamnan Arewa Ya Gwangwaje 'Yan Majalisa da Alkalai da Motocin Alfarma 44, Ya Fadi Dalilinsa
- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ba da kyaututtukan motocin alfarma ga 'yan Majalisun jihar da alkalai
- Gwamnan ya raba motocin alfarma guda 40 da mota kirar 'Hilux' guda hudu don saka musu da irin bautar da suka yi
- Gwamnan ya gabatar da wannan kyautar ce a jiya Juma'a 22 ga watan Disamba a birnin Lokoja da ke jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya gwangwaje 'yan Majalisar jihar da kuma Alkalai motocin alfarma.
Yahaya Bello ya ba su motocin alfarma guda 40 sa kuma mota kirar 'Hilux' guda hudu, kamar yadda Punch ta tattaro.
Yaushe gwamnan ya raba motocin a Kogi?
Har ila yau, gwamnan ya ba da kyautar motar daukar marar lafiya guda 25 ga kananan hukumomi a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya gabatar da wannan kyautar ce a jiya Juma'a 22 ga watan Disamba a birnin Lokoja da ke jihar, cewar Leadership.
Bayan haka, Gwamna Bello ya mika kyautan motocin kashe gobara guda uku ga hukumar don taimakawa wurin kawo dauki yayin gobara.
Mene dalilin gwamnan na raba motocin?
Kakakin Majalisar jihar, Umar Yusuf ya samu kyautar motocin alfarma guda uku yayin da mataimakinsa da sauran mambobin guda 22 suka samu guda dai-dai.
Har ila yau, daga cikin motocin, an ware guda tara don raba su a bangaren shari'a ga alkalan jihar, cewar Daily Post.
Da yake raba motocin a wurin taro na Muhammad Buhari da ke Lokoja, Bello ya ce ya yi hakan ne don saka musu da ayyukan da suke yi.
Yahaya Bello ya sake kirkirar sabuwar ma'aikata
A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya sake kirkirar sabuwar ma'aikata ana saura kwanaki kadan ya bar mulki.
Bello ya kirkiri ma'aikatar jin kai da walwalar jama'a don rage wa 'yan jihar kuncin talauci da suke fama da ita.
Wannan na zuwa ne ana saura kwanaki kadan ya bar kan karagar mulkin gwmnan jihar bayan gudanar da zaben gwamna a jihar.
Asali: Legit.ng