Hotuna Sun Bayyana Yayin da Alkaliyar da Yan Bindiga Suka Sace Ta Kubuta, Gwamna Ya Aike da Gargadi

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Alkaliyar da Yan Bindiga Suka Sace Ta Kubuta, Gwamna Ya Aike da Gargadi

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun sako alƙaliyar da aka sace a jihar Akwa Ibom, mai shari'a Joy Unwana
  • Wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar ta tabbatar wa manema labarai kuɓutar alƙaliyar wacce aka sace ranar Litinin
  • Gwamna Umo Eno wanda ya mayar da martani kan wannan lamari, ya godewa jami’an tsaro da suka tabbatar da tsaron lafiyarta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Uyo, Akwa Ibom - An sako alƙaliyar kotun jihar Akwa Ibom, mai shari’a Joy Unwana, bayan an sace ta a daren ranar Litinin.

A wata sanarwa da ta fito daga gidan gwamnatin jihar dake Uyo, Mai shari’a Unwana, wacce ta haɗu da Gwamna Umo Eno, ta godewa Allah da ya sa ta kuɓuta lafiya, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin jihar Sokoto ta kamo hanyar magance matsalar tsaro a jihar bayan ta yi wani abu 1

Alkaliyar jihar Akwa Ibom ta kubuta
Gwamna Uno ya tabbatar da kubutar alkaliyar da aka sace Hoto: Governor Umo Eno
Asali: Twitter

Gwamna Eno ya godewa jami’an tsaro bisa gaggawar ɗaukar matakin da suka yi tare da jajircewa wajen sauke nauyin da ke kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Eno ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen ganin jihar ta kasance inda masu aikata laifuka ba za su iya zama ba.

Sakon Gwamna Eno ga hukumomin tsaro

Ya buƙaci jami’an tsaro da su ƙara zage damtse wajen sanya ido domin kare rayuwar ƴan kasa, rahoton TVC ya tabbatar.

Gwamnan ya miƙa godiyarsa ga ma’aikatar tsaron cikin gida bisa yadda suke ba da hadin kai da kuma amfani da bayanan sirri na cikin gida wajen magance matsalolin tsaro.

A yayin da yake nuna juyayi kan ƙalubalen da alƙaliyar ta fuskanta, Gwamna Eno ya tabbatar mata da cewa Allah ya kiyaye rayuwarta kuma Allah zai bi mata haƙƙinta.

Da yake ƙarin haske da cewa har yanzu tsaron jihar gaba ɗaya yana nan daram, ya kara da cewa lamarin na baya-bayan nan koma baya ne, kuma za a yi hukunci mai tsauri, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata hakan sun fuskanci hukunci mai tsauri.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta faɗi lokacin da za ta kawo ƙarshen yan bindiga a Najeriya, ta ce In Sha Allah

Wane hali alƙaliyar ta shiga?

Mai shari’a Unwana ta yaba da damuwar gwamnan ya nuna da ƙoƙarin ceto ta.

Ta ba da labarin halin da ta tsinci kanta a ciki, inda ta yi fatan ba wanda zai tsinci kansa cikin irin wannan yanayi mai ban tsoro.

Ƴan Sanda Sun Ceto Mutanen da Aka Sace

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan sanda a jihar Taraba sun samu nasarar ceto mutum 23 da ƴan bindiga suka sace.

Ƴan sandan sun samu wannan nasarar ne bayan sun yi musayar wuta da ƴan bindigan waɗanda suka sace mutanen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng