Ministan Tinubu Ya Dauki Muhimmin Alwashi Kan Kawo Karshen Ta'addanci a Kasar Nan

Ministan Tinubu Ya Dauki Muhimmin Alwashi Kan Kawo Karshen Ta'addanci a Kasar Nan

  • Ma’aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ta ƙasa ta tattauna da rundunar Sojin Najeriya domin taimakawa wajen daƙile matsalar rashin tsaro
  • Minista Mohammed Idris ya karɓi baƙuncin babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Christopher Musa wanda ya kai ziyarar ban girma
  • A zaman tattaunawa da manema labarai, CDS Musa ya bayyana cewa ƴan ta'adda 140,000 ne suka miƙa wuya bisa raɗin kansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na ƙasa, Mohammed Idris, ya yi magana kan hanyayoyin magance ta'addanci a Najeriya.

Ministan ya jaddada cewa ƙarfafa kishin ƙasa wata muhimmiyar dabara ce ta magance tare da rage munanan laifuka kamar ayyukan ƴan bindiga, garkuwa da mutane, da ta'addanci a cikin ƙasa.

Kara karanta wannan

Ana dab da Kirsimeti Shugaba Tinubu ya aike da sako mai ratsa zuciya ga yan Najeriya

Lokacin karshen yan ta'adda ya kusa zuwa
Ministan yada labarai ya gana da CDS Musa
Asali: Twitter

Idris ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja, a wata ziyarar ban girma da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa ya kai a ranar Juma’a, 22 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya bayyana muhimmancin cusa kishin ƙasa a cikin ƴan kasa da kuma samar da kwarin gwiwar ƴan ƙasa domin haɗa kai wajen yaƙi da miyagun ayyuka.

"Dole ne mu koma mu zauna mu ga inda muka samu kuskure da nufin daidaita shi a wannan karon." A cewarsa.

Idris ya jaddada cewa mummunan tasirin munanan laifuka ya yi matuƙar illa ga martabar Najeriya, don haka ma’aikatar ce ke da alhakin gyarawa da kuma kyautata tunanin ƙasar.

Ƴan ta'adda 140,000 sun miƙa wuya - CDS Musa

Janar Musa ya jaddada cewa ganawar tasu da ministan wani ɓangare ne na ƙoƙari inganta hadin gwiwa tsakanin sojoji da ƴan jarida.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan ƙarancin takardun Naira, ta nemi afuwa

A kalamansa:

"Wannan wani bangare ne na ayyukan da muke gudanarwa don samar da haɗin kai tsakanin rundunar soji da jama'a kuma babu inda za a fara da ya fi inda bayanai ke fitowa."

Janar Musa ya bayyana muhimmancin dabarun sadarwa wajen yaƙar ta’addanci, inda ya nuna cewa ƴan ta’adda da dama an yi musu huɗubar ƙarya wajen sanya su ɗaukar makamai a kan ƙasarsu.

Ta hanyar dabarun sadarwa da bayar da shawarwari, sojoji sun yi nasarar shawo kan wasu ƴan ta'adda da su miƙa wuya, inda kusan mutum 140,000 suka miƙa wuya da kansu.

Jami'an Tsaro na Buƙatar Addu'a - Badaru

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro, Abubakar Badaru, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su cigaba da yi wa gwamnati mai ci addu’a, musamman masu rike da muƙaman tsaron ƙasa.

Badaru ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wakilan gwamnayin jihar Jigawa a ofishinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng