Bankin CBN Ya Janye Dokar da Ya Kakabawa Masu Kasuwancin ‘Cryptocurrency’ a Najeriya
- Babban Bankin Najeriya (CBN) ya janye dokar da ya kakabawa masu hada-hadar sulallan 'crypto' tare da ba bankunan umurni kan hakan
- Idan ba a manta ba tun a shekarar 2021 babban bankin ya haramta wa 'yan Najeriya tu'ammali da sulallan saboda zargin 'rashin tabbas' na kasuwar
- Sai dai a sabon hukuncin da ya yanke, CBN ya ce kasuwancin 'crypto' ya zama ruwan dare, don haka akwai bukatar a kyale 'yan kasar a dama da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya canja matsayarsa kan haramta kasuwancin sulallan yanar gizo 'cryptocurrency' a Najeriya wanda ta dauka tun daga 2017 zuwa 2021.
Babban bankin a ranar Juma'a ya ce ya janye dokar haramcin hada-hadar sulallan a fadin kasar kuma ya nemi bankuna su daina rufe asusun masu harka da 'crypto'.
Wannan na dauke ne a cikin wata sanarwa mai kwanan wata 22 ga watan Disamba, 2023, da kuma lambar takarda FPR/DIR/PUB/CIR/002/003 dauke da sa hannun daraktan sashen tsara kudi, Haruna Mustafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar mai taken 'sanarwa ga duk bankuna da hukumomin hada-hadar kudi kan sabon sharadin amfani da asusun bankuna don kasuwanci a yanar gizo (VASPS).'
Abin da CBN ke nufi da janye dokar haramta 'crypto'
Babban bankin ya bayyana cewa yanzu duniya ta karkata kan amfani da 'crypto', wanda ya zama wajibi ya amince da hakan tare da saka ido kan kasuwancinsa, Daily Trust ta ruwaito.
A cewar bankin:
"A shekarar 2021 CBN ya haramtawa bankuna da hukumomin hada-hadar kudade barin masu kasuwancin 'crypto' yin amfani da asusun bankunansu wajen hada-hadar sulallan.
"Sai dai la'akari da cewa kasuwancin 'crypto' ya zama ruwan dare, akwai bukatar janye wannan doka tare da kawo tsarin da zai aka ido don tabbatar da tsaftace harkar."
A baya dai, babban bankin ya ba dukkan bankuna umurnin gano masu kasuwancin 'crypto' tare da rufe asusunsu saboda dokar hana kasuwancin sulallan da ta saka.
Rahoton The Cable ya ce CBN ya tabbatar da matsayarsa kan cewa bankuna da hukumomin hada-hadar kudi ba za su iya yin amfani da asusunsu don yin kasuwancin sulallan 'crypto' ba.
Amurka ce ta gargadi CBN kan amfani da 'crypto' da ake yi a Najeriya
A baya Legit ta taba ruwaito maku cewa hukumar tsaron kasar Amurka (FBI) ce ta yi wa gwamnatin tarayya korafi akan yadda 'yan Najeriya ke amfani da 'crypto' wajen damfarar kasashen turai.
FBI ta sanar da gwamnatin tarayya cewa miliyoyin daloli daga kasashen nahiyar turai na shigowa Nigeria ta hanyar 'crypto', wanda hakan kan iya haifar da babbar matsala ga tattalin arfzikin kasa.
Asali: Legit.ng