An Bankado Manyan Abubuwa 2 da Suka Jawo Karancin Takardun Naira a Hannun ’Yan Najeriya
- Kungiyar ASSBIFI ta gano wasu dalilai guda biyu da suka jawo ake samun karancin takardun naira a tsakanin 'yan Najeriya a 'yan tsakanin nan
- Shugaban kungiyar ASSBIFI na kasa, Olusoji Oluwale ya ce fargaba ta saka wasu kwastomomi cire kudade barkatai saboda gudun komawa gidan jiya
- Ya kuma ce sun gano wasu bata gari da ke boye tsabar kudade masu yawa don cimma wata manufarsu wanda ke kawo karancin takardun kudin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Legas - Kungiyar manyan ma'aikatan bankuna, hukumomin inshora da hada-hadar kudi (ASSBIFI) ta ce fargaba da cire kudi masu yawa daga banki ya jawo karancin takardun naira.
Shugaban kungiyar ASSBIFI, Olusoji Oluwale, a cikin wata sanarwa ya ce kwastomomi na cire kudi barkatai don fargabar komawa cikin kunci da wahalar da aka shiga shekarar da ta gabata.
Fargaba da son kai suka jawo karancin takardun naira - ASSBIFI
Ya kuma alakanta karancin takardun naira da mugun halayen wasu bata gari, wadanda ke boye kudi don cimma wata manufarsu, wanda hakan ke jefa mutane a wahala saboda karancin kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da ya ke yin gargadi ga masu irin wannan mugun hali, Oluwole ya ce bai kamata jama'a su rinka cire kudin da sun san ba amfani za su yi da su ba saboda suna jin tsoro kawai, rahoton Vanguard.
Ya ce:
"Babu bukatar yin fargaba yanzu, babban bankin Najeriya ya sanar da ci gaba da amfani da tsaffin takardun Naira, don haka mutane su guji cire kudi barkatai saboda tsoron komawa gidan jiya."
NAN ya ruwaito Oluwole na neman mambobin kungiyar da su zamo masu aiki tukuru yayin da CBN ke aiki da bankuna don wadatar da takardun kudi a hannun 'yan Najeriya.
Gwamnati za ta saki sunayen wadanda za su amfana da tallafin N50,000
A wani labarin, Betta Edu, ministar jin kai da kawar da fatara ta yi alkawarin wallafa sunayen wadand za su ci gajiyar shirin shugaban kasa na naira dubu hamsin.
Gwamnatin Tinubu ta kawo wannan shiri don rage wa 'yan Najeriya radadin cire tallafin man fetur, musamman talakawa, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng