Jimami Yayin Da Mahaifiyar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ta Rasu Ta Na Da Shekaru 103

Jimami Yayin Da Mahaifiyar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ta Rasu Ta Na Da Shekaru 103

  • An shiga jimami bayan mahaifiyar tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara a yau Juma’a 22 ga watan Disamba
  • Marigayiyar, Mama Saratu Yakubu Tukur ta rasu ne a yau Juma’a 22 ga watan Disamba ta na da shekaru 103
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon kakakin Majalisar ya fitar a yau Juma’a inda ya ce za a sanar da ranar bikin binne ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi – Mahaifiyar tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ta riga mu gidan gaskiya.

Marigayiyar, Mama Saratu Yakubu Tukur ta rasu ne a yau Juma’a 22 ga watan Disamba ta na da shekaru 103.

Mahaifiyar tsohon kakakin Majaisa ya riga mu gidan gaskiya
Marigayiyar ta rasu ne a yau Juma'a ta na da shekaru 103. Hoto: Hon. Yakubu Dogara.
Asali: Facebook

Yaushe Dogara ya sanar da rasuwar mahafiyar tasa?

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya bai wa Farfesa Jega shirgegen mukami a jiharsa, bayanai sun fito

Tsohon kakakin Majalisar shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a 22 ga watan Disamba, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dogara ya ce mahaifiyar tasu ta rasu ta na da shekaru 105 a duniya a yau Juma'a 22 ga watan Disamba.

Sanarwar ta ce:

“Cikin godiya da kuma jimami ina sanar da rasuwar mahaifiyarmu, Mama Saratu Yakubu Tukur a yau Juma’a 22 ga watan Disamba.
“Marigayiyar ta rasu ta na da shekaru 103 inda muke da tabbacin marigayiyar ta yi aiki tukuru da kuma bautar ubangiji.”

Yaushe za a yi bikin binne mahaifyar Dogara?

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da lokacin bukukuwan binne ta, cewar Tribune.

Dogara ya jagoranci Majalisar Wakilai daga shekarar 2015 har zuwa shekarar 2019 kafin Femi Gbajabiamila ya ci gaba jagorantar Majalisar daga 2019 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

An cafke matasa 5 kan mallakar bindigu a kauyen Katsina, yadda su ka samu makamin ya ba da mamaki

Tsohon kakakkin Majalisar ya wakilci mazabar Dass/Bogoro/Tafawa Balewa da ke cikin jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin kasar.

Mahaifin Ministan Buhari ya rasu

A wani labarin, Mahaifin tsohon Ministan Wasanni da Matasa, Solomon Dalung ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin Nimgbak William Fabong Dalung ya rasu ya na da shekaru 105 bayan fama da doguwar jinya.

Wannan na zuwa ne yayain iyalan Dalung ke shirye-shiryen bukukuwan binne mahaifiyar tsohon Ministan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.