Gwamnatin Tarayya ta Bada Hutun Bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara

Gwamnatin Tarayya ta Bada Hutun Bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara

  • Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu ta bayar da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara
  • FG ta ayyana 25 da 26 ga watan Disamban 2023 a matsayin hutun bikin Kirsimeti sai 1 ga watan Janairu 2024 a matsayin na Sabuwar shekara
  • Ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo ya taya Kiristoci da daukacin yan Najeriya murnar wadannan bukukuwa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, da Talata, 25 da 26 ga watan Disamba 2023 a matsayin hutun bikin Kirsimeti.

Haka kuma, gwamnatin ta sake ayyana ranar 1 ga watan Janairun 2024 a matsayin hutu don bikin sabuwar shekara, rahoton Punch.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutun kirsimeti
Gwamnatin Tarayya ta Bada Hutun Bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya ya taya Kiristoci da daukacin yan Najeriya na gida da waje murnar wannan biki.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rabawa ma'aikata N100,000 don bikin kirsimeti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku yi koyi da koyarwar Yesu, minista ga kiristocin Najeriya

Dr Tunji-Ojo ya bukaci Kiristoci da su yi koyi da rayuwar Yesu da koyarwarsa na jin kai, tausayi da hakuri.

Ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro sune muhimman abubuwan da ake bukata don bunkasa tattalin arziki da wadata.

Ministan ya bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da samar da ingantattun matakai na tsaron rayuka da dukiyoyi.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu lura da tsaro, kuma su kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da basu yarda da shi ba ga hukumomin tsaro mafi kusa.

Ya jaddada cewar lokacin bikin na kira ga da'a don kare rayuka da dukiyoyin al'umma da kasa baki daya, rahoton Nigerian Tribune.

Tunji-Ojo ya yi kira ga daukacin yan kasar da su ci gaba da mai da hankali kan cewa, shekarar 2024 za ta inganta da ajandar shugaban kasar na sabonta fata.

Kara karanta wannan

Hukumar NRC ta sanar da fara jigilar yan Najeriya kyauta saboda bikin Kirsimeti da sabuwar shekara

Gwamnatin Tinubu ta gwangwaje yan Najeriya

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta saki jerin garuruwan da matafiya za su iya samun ragin kaso 50 cikin dari na kudin mota.

Wannan ya yi daidai da alkawarin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na rage kudaden motar zuwa garuruwa da kaso 50 yayin da matafiyan da ke amfani da jirgin kasa za su shiga a kyauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng