Abba Gida-Gida Ya Ware Naira Biliyan 15.97 Don Yin Wasu Manyan Ayyuka 2 a Kwaryar Jihar Kano
- A shirinta na bunkasa tattalin arziki da inga rayuwar jama'a, gwamnatin jihar Kano ta ware naira biliyan 15.97 don gina manyan gadojin sama guda biyu
- Majalisar zartaswar jihar ta amince da ayyukan da za a yi a sha tale-talen Dan-Agundi da Tal'udu don rage cunkoso a manyan titunan
- Gwamnatin jihar ta ba kamfanin Messrs CGC Nigeria Limited kwangilar gina gadojin, inda kuma ta ba tabbacin kammala aikin ba da bata lokaci ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta ba da kwangilar gina manyan gadojin sama guda biyu sha tale-talen Dan-Agundi da Tal'udu, wanda zai lakume naira biliyan 15.97.
Kwamishinan watsa labarai da harkokin cikin gida, Malam Baba Dantiye ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a a Kano.
Dantiye ya ce majalisar zartaswar jihar a zaman da ta yi na bayan nan ta amince da gina manyan gadojin don rage cunkoso, bunkasa kasuwanci da hada-hadar al'umma a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin jiha da kananan hukumomi za su hada kudin aikin
Kwamishinan ya yi nuni da cewa kamfanin Messrs CGC Nigeria Limited ne aka ba kwangilar akan naira biliyan 15.97 wanda za a cire daga asusun jiha da kananan hukumomi, rahoton Leadership.
Ya ce:
"Gwamnatin jiha ta na ba al'umma tabbacin aiwatar da ayyukan biyu ba tare da bata lokaci ba, kuma gwamnati za ta yi wasu ayyuka a birni da karkara don bunkasa rayuwar al'umma."
Daily Nigerian ta ruwaito Dantiye na shawartar matafiya da ke bin hanyayoyin da za a yi aikin da su yi amfani da wasu hanyoyin da daban har zuwa kammala aikin.
Majalisar dokokin Kano ta yi wani abu da ya faranta ran Abba Gida-Gida
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naira biliyan 437.5 matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2024.
Idan za a iya tunawa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya gabatar da naira biliyan 350 matsayin kasafin kudin a ranar 27 ga watan Oktoba.
Kakakin majalisar jihar, Jubril Ismail Falgore, ya ce an kara kasafin kudin daga naira biliyan 350 uwa naira biliyan 437.3 saboda magance wasu bukatu na jama'a.
Asali: Legit.ng