FEC: Za a batar da N117.66bn domin a gina tituna da gadoji a Katsina, Kano, dsr

FEC: Za a batar da N117.66bn domin a gina tituna da gadoji a Katsina, Kano, dsr

-Shugaba Muhammadu Buhari zai kashe N117b domin aikin tituna da gadoji

-Za a yi wadannan ayyuka ne a jihohin Kano, Katsina, Kebbi, Anambra, dsr

-Bayan haka FEC ta amince a batar da N470m a kan manhajar bankin FMB

A taron majalisar FEC da aka yi na ranar 2 ga watan Disamba, 2020, an cin ma matsaya cewa za a kashe N117.661b wajen ginin tituna da gadaje a wasu jiihohi.

Mai girma Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Babatunde Raji Fashola SAN, ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministan ya na cewa za a kashe N8.7b daga cikin wadannan kudi domin gyaran babban titin nan na Kano-Kazaure-Daura-Mai’adua.

Bayan haka, Raji Fashola ya ce majalisar FEC ta amince da aikin gyaran wasu tituna da su ka hada da na Omor-Umulokpa da Oye-Oranto a kan N1.712b da N2.5b.

KU KARANTA: Buhari zai bayyana a gaban Majalisa - Gbajabiamilla

Duk a jiya Laraba, Ministoci sun yi na’am da bada kwangilar gadar Okpokwu da ke kan titin Ogoja-Okuku-Aliforkpa-Benue a Kuros Riba a kan kudi N1.06b.

Ministan yace an amince da aikin titin Bida-Zungeru a jihar Neja wanda zai ci N1.02b. Tsakanin jihohin Abia da Enugu, za ayi aikin gadar Nkwumi a kan N1.07b.

Gwamnatin tarayya ta kuma amince da aikin titin Chalawa-Runku-Sawa-Kayi a Kumbotso, Kano.

Sauran ayyukan da majalisar ta amince da su sun hada da titin Riga-Gusau a Zamfara, hanyar Jigakwana da kuma dogon titin Kokomo Auta duk a jihar Kebbi.

KU KARANTA: Okorocha ya ba Buhari shawara ya sallami duka Mukarrabansa

FEC: Za a batar da N117.66bn domin a gina tituna da gadoji a Katsina, Kano, dsr
Ministan ayyuka da gidaje Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Akwai kuma ayyukan titin Kuka Babangida, Ihiala-Orkula-Umuduru, Oye Ama Otite-Umuawulu, da gyaran hanyar Bichi, kamar yadda Ministan ya bayyana a jiya.

Fashola ya ce FEC ta amince da aikin manhajar bankin gidaje, FMB a kan kudi N487.394,285.71. Ministan ya bayyana irin amfanin wannan manhajar da za a gani.

A baya kun ji yadda wani bincike ya nuna shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai bi doka da zai zaben Iman Sulaiman Ibrahim a matsayin shugabar NAPTIP ba.

Iman Sulaiman Ibrahim ta na Digiri biyu, amma ba ta cika sharudan rike hukumar tarayyar ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel