Waiwaye Ga 2023: Manyan Shugabannin Yan Ta'adda 5 da Aka Halaka a Shekara Mai Karewa

Waiwaye Ga 2023: Manyan Shugabannin Yan Ta'adda 5 da Aka Halaka a Shekara Mai Karewa

A shekarar 2023 dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarin da suke yi na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a ƙasar nan.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

A yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda da ƴan bindiga, sojojin sun halaka manyan shugabannin ƴan bindiga waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen aikata ayyukan ta'addanci, musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Sojoji sun halaka manyan shugabannin yan bindiga
Dakarun sojoji sun halaka manyan shugabannin yan bindiga a 2023 Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Legit Hausa ta yi duba kan manya shugabannin ƴan ta'addan da aka halaka a shekarar 2023.

1. Dogo Gudali

Ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya addabi al'ummar jihar Zamfara, Dogo Gudali, ya mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yan majalisa na son FG ta amince a rika cinikayya da Yuan na kasar Sin, sun bayar da dalilansu

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Gudali ya yi bankwana da duniya ne sakamakon tashin bam da wasu mambobin kungiyarsa ta ta'addanci suka ɗana.

Ƴan ta'addan dai sun ɗana bam ɗin ne domin kawar da dakarun rundunar soji na Operation Hadarin Daji, waɗanda ke aikin kakkaɓa a dajin Gando da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

2. Isiya Danwasa

Dakarun rundunar Operation Forest Sanity (OPFS) sun kashe ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Isiya Danwasa, a jihar Kaduna.

Zagazola Makama ya rahoto cewa kafin halaka Ɗanwasa, ya yi ƙaurin suna wajen aikata kashe-kashe da dama, garkuwa da mutane da satar shanu.

Ƙasurgumin ɗan bindigan ya haɗu da ajalinsa ne yayin wani kwantan ɓauna da sojoji suka yi masa a Sabon Birni da ke ƙaramar hukumar Igabi.

3. Ali Kachalla Kawaje

Ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga Ali Kachalla Kawaje ya gamu da ajalinsa a hannun dakarun sojoji, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ragargaji yan bindiga, sun ceto mutanen da suka sace

Dakarun sojojin sun halaka Kachalla ne a wani farmakin haɗin gwiwa tsakanin sojojin sama da na ƙasa da suka kai hari a ranar 11 ga watan Disamban 2023.

Kachalla wanda ya yi garkuwa da ɗaliban jami’ar tarayya ta Gusau, Zamfara, ya gamu da ajalinsa ne a ƙaramar hukumar Munya ta Nijar tare da wasu dakarunsa.

4. Yellow

Mafarauta sun samu nasarar halaka fitaccen shugaban ƴan bindiga da aka fi sani da ‘Yellow’ a masarautar Zuru ta Danko/Wasagu da kewaye a jihar Kebbi.

An halaka Yellow ne tare da wasu ƴan ƙungiyarsa a wani samamen haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai a yankin Danko/Wasagu na jihar.

Yellow ya yi ƙaurin suna wajen aikata laifukan fyaɗe, garkuwa da mutane da halaka mutane da ba su ji ba, ba su gani ba a yankin.

5. Ibrahim Kachalla Gudau

Dakarun sojoji sun samu nasarar halaka ƙasurgumin shugaban ƴan ta'adda Ibrahim Kachalla Gudau, a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke dan bindiga sun kwato muggan makamai a Kaduna

Gudau ya shahara wajen jagorantar ƴan ta'adda kai hare-hare, yin garkuwa da mutane da kashe-kashe a Kaduna, Katsina, Zamfara da kuma wani ɓangare na Jamhuriyar Nijar.

Gudau ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da dakarun sojoji suka daƙile wani harin da ƴan bindiga suka kai musu a ƙauyen Kankami da ke jihar Kaduna.

Dakarun Sojoji Sun Sheƙe Ɗan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe wani ɗan bindiga a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato muggan makamai a yayin wani artabu da suka yi da ƴan bindigan a ƙauyen Sabon Birni, da ke ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng