Kotu Ta Garkame Matasa 2 Kan Kashe Abokinsu Saboda Shinkafa
- Abokai biyu sun kashe abokinsu saboda buhunan shinkafa 36 sannan suka siyar don samun kudi
- Sun farmaki abokin nasu a jirgin ruwa sannan suka jefar da shi a ruwa, sun kwashe shinkafarsa zuwa wani gari sannan suka siyarwa wani
- Kotu ta yi umurnin garkame su a gidan gyara hali har zuwa lokacin da bangaren DPP zai yanke hukunci a kansu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Rajay Zannu da Noah Tovohome sun gurfana a gaban kotun majistare da ke Lagas bayan zarginsu da kisan wani abokinsu, Segun Zusu, kan buhunan shinkafa 36.
Kotun ta garkame matasan biyu bayan an zarge su da hada kai da wani direban tasi wajen farmakar Zusu, inda suka sace buhunan shinkafan yayin da yake shigowa da su daga Seme, iyakar shigowa Najeriya, rahoton Nigerian Tribune.
Lamarin ya faru ne a kogin Novo, inda wadanda ake zargin suka kashe aminin nasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce sun yi masa dukan tsiya, inda suka sumar shi kafin suka jefa shi cikin kogin. Sun raba kudin a tsakaninsu da direban tasi din, wanda ya tsere har zuwa yanzu.
Dan sanda mai kara, Chekwube Okeh ya bayyana cewa laifin ya ci karo da sashi na 222 kuma hukuncinsa na karkashin sashi na 223 na kundin dokar jihar Lagas 2015.
Wani hukunci kotu ta yanke?
Kotun ta ki amsa rokon wadanda ake zargin ba.
Okeh ya bukaci kotun da ta tura su gidan gyara hali zuwa lokacin da za a ji shawara daga hukumar kula da kararrakin jama’a.
Da jin nauyin tuhumar da ake masu, kotun ta garkame Zannu da Tocohome a gidan gyara hali na Kirikiri yayin da take jiran shawarar bangaren DPP din, Daily Post ta rahoto.
An sako wani bayan shekaru 48 a magarkama
A wani labarin kuma, mun ji cewa an sako wani mutum daga gidan yari bayan an tabbatar da bai aikata laifin da aka hukunta shi a kansa ba.
An hukunta mutumin mai suna Glynn Simmons a 1973 kan kisan Carolyn Sue Rogers, amma a kodayaushe ya kan sanar da cewar bai aikata ba.
Asali: Legit.ng