Gwamnan APC Ya Bai Wa Farfesa Jega Shirgegen Mukami a Jiharsa, Bayanai Sun Fito
- Farfesa Attahiru Jega ya samu babban mukami na uban Jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi
- Tsohon shugaban INEC a baya ya rike mataimakin shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano da shugaban kungiyar ASUU
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Mista Aliyu Ubandoma ya fitar a yau Alhamis 21 ga watan Disamba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Nasarawa – Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya nada Farfesa Attahiru Jega mukamin a jiharsa.
Sule ya nada tsohon shugaban hukumar INEC din ne mukamin uban Jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi.
Yaushe aka nada Jega uban Jami’ar a Nasarawa?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Mista Aliyu Ubandoma ya fitar a yau Alhamis 21 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jega ya taba rike mukamin mataimakin shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano da kuma shugaban kungiyar ASUU a Najeriya.
Ubandoma ya ce wannan nadin an yi shi ne don kara inganta harkar ilimi a jihar baki daya, cewar Daily Trust.
Wasu Karin nade-nade a ka yi a Jami’ar ta Nasarawa?
Ya ce gwamnan ya kuma amince da nadin Mista Shu’aibu Kore da Mista Thomas Ogiri da Mary Enwongulu a matsayin mambobin kwamitin gudanarwar makarantar.
Ya kara da cewa za a kaddamar da kwamitin gudanarwar makarantar nan ba da jimawa ba a jihar, cewar Leadership.
Tsohon shugaban INEC din shi ya jagoranci hukumar a 2015, shekarar da jam’iyyar adawa da kwace mulki a hannun jam’iyya mai ci a tarihi.
Jega ya bukaci a sauya tsarin zaben shugaban INEC
A wani labarin, Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya tura muhimmin sako ga Shugaba Tinubu.
Jega ya ce bai kamata a ce shugaban kasa ba ne ya ke zaban shugaban hukumar INEC don gudun zargi.
A Najeriya, ana zargin hukumar INEC da sauya alkaluman zabe ga shugaban da ya zabe su don gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.
Asali: Legit.ng